
Tarihinmu Abin Alfahari
Tare da
Malam Fatihu Mustapha
Wata mahaukaciya CE ta iske wata bahillata, a gefen titi tana saida nono. Tazo ta tsaya akan bahillatan nan, tana rike da wata katuwar sanda a hannunta, tana muzurai. Bahillatan nan tana ganin ta ta tsorata. Hankalinta ya tashi.
Mahaukaciya na muzurai, ta daga gora, ta kalli bahillatan nan, ta ce mata “nawa kwaryar nono! Bahillata a tsorace ta ce ” naira guda” mahaukaciya ta ce “zuba kwarya daya” nan da nan bahillata ta zuba, mahaukaciya ta kalleta ta ce “dauki ki shanye” nan da nan Bahillata ta kafa kai ta shanye.
Ta kara ce mata kara zuba wata kwaryar” ta zuba, mahaukaciya ta kara cewa “dauki ki shanye” tana gyara gorarta kamar zata bugawa bahillata. Nan da nan Bahillata ta shanye.
Haka suka yi, sai da Bahillata ta shanye kusan rabin nonon. Sannan mahaukaciya ta kalleta ta ce mata “munafuka, ana so ana kaiwa kasuwa”. Mahaukaciya ta kama gabanta, ta bar Bahillata a tsugunne, tana taajibi, kamar shanun Maimuna Bello sun bata.
Anan aka samu asalin Karin magnar ” Ana so ana kaiwa Kasuwa”

