Home Labarai Zuwa ga Maigirma Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Zuwa ga Maigirma Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.

by masta

Daga Nasir Ahmad Sadik

Malam Abba Kabir Yusuf
Barka da hantsi, Maigirma Gwamna. Ya aka ji da faman yaƙin gyara kayanka. To Allah ya ci gaba da dafa maka.

2. Gwamna yau ma na hango wani hangamemen rami da tayar motar gwamnatinka ta ɗan daka. Har na ji tayar tana daka. Alamun anyi bulli. Kuma idan aka ci gaba da tuƙi a haka ba a tsaya an duba an gyara ba…tom!

3. Magana nake game da kuɗi da aka rabawa Alhazai mutan Makka. Wato abin da akai na basu dubu goma-goma. Al’amarin nan, Gwamna yayi kama da ace ka siyowa ‘ya’yan wani abokinka mawadaci alawa cakulet ne, don idan sun ci abinci sun ƙoshi su tsotsa su gyara harshe. A gefe guda kuma ga almajirin gidanka yana haki yunwa zata cimmai. Ƙwarai kuwa, Maigirma Gwamna!

4. Akwai ɗalibai ‘yan asalin jihar Kano dake karatu a jami’ar Bayero da sauran jami’o’in dake yunƙurin korar talaka daga cikinsu don karin kuɗin makaranta. Na so ace ka lura zai fi kyautuwa a duba yiwuwar basu Subsidy na kuɗin makarantar ko da na wannan shekarar ne tunda abin yazo musu a ƙure ba kowa ne a cikinsu zai iya samu waɗannan kuɗaɗe ya biya kafin a koma makaranta ba. Hakan zai basu dama su samu su koma su ci gaba da karatu idan yaso baɗi sai a basu regular scholarship ɗin da aka saba basu, maimakon a ƙarawa mai ƙarfi karfi.

5. Ta Mamman fa, Gwamna, bata da tsayi. ‘Ya ɗul haka take -maganar. Amma fa mai amfani ce. Miliyan 65 idan aka ƙara 35 akai zasu iya baiwa ɗaliban nan koda kaso 40 ne cikin ɗari na ƙarin da akai musu. Su kuma su yi fafutukar neman ragowar. Ka ga mai biyan dubu 40 a baya yanzu zai biya 110. Idan ka biya masa dubu 50, 20 zai nema ya ƙara akan tsohon kuɗin makaranta ya biya. Alabishi baɗi sai asan me ya kamata a yi don a ci gaba da tallafa musu ko da da kaso 30 ne.

6. Wataƙila kace ai aikin gama ya gama tunda waccan miliyan 65 su Alhaji sun dafe ta. Eh! ina nufin suma su Ƙolo da Titiɓiri ai sun san aljihun gwamnati maliya ce; teku baki ƙafewa duk rani. A tallafa a duba Gwamna. Kuma a yi haƙuri Mamman. Ƙauna ce tasa yake haska maka hanya. Bakwankwashe ne asalan.

Bari na koma gefen Ranji.
A tashi lafiya.

Mamman Naso

Related Posts

Leave a Comment