Home Labarai Jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a Yau yayin Hawan Nasarawa a gidan Gwamnatin Jihar Kano

Jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a Yau yayin Hawan Nasarawa a gidan Gwamnatin Jihar Kano

by masta

Daga
Muhammad Yusuf Ali

Mai martaba Sarkin Kano ya yi jawabi Mai Ratsa zuciya da nuna kyakkyawan fatansa ga jihar ta Kano inda yake cewa “Gwamnati ta mayar da hankali wajen kokarin sauke nauyin da Allah ya dora musu na mulkar al’umma.

Gwamnati ta mayar da hanakli da kuma kara nazari akan zakulo hanyoyi da za’a kyautatawa al’umma domin talakawan ta suna cikin wani hali na talauci.

Gwamnati jahar Kano ta nemo hanyar da zata rage radadi na yanayin da ake ciki na sanadiyar cire tallafin mai fetur da akayi wanda hakan yakara jefa talakawa cikin kunci.

Gwamnati ta sani hakkin al’umma ne akanta kuma al’umma take mulka saboda haka gwamnati tayi kokari wajen hidimtawa al’umma ta bangarori da ya dace.

In sha Allah zamu same mu cikin masu baku shawarwari nagari da Addu’a a cikin ayyukan gwamnati masu mahimmanci.

Muna kara mika lamuranmu ga Allah da kuma yi masa godiya cikin dukkan lamuranmu.

Abunda yafi kara burge ni a jawabin mai martaba sarkin Kano shine: bai yi alkawarin zasu yi gwamnati biyayya akan duk irin tsarin da zo dashi ba, sai dai za suyi mata adduar Allah yasa su kyautatawa al’umma da kuma kawo cigaba a jahar Kano baki daya.
Allah ya Kara wa Sarki lafiya Allah ya Kara wa kano lafiya da zama lafiya da karuwar arziki, Amin.

Related Posts

Leave a Comment