Home Labarai An ajiye kwarya a gurbinta: nada Farfesa Kabir Matazu mni a matsayin babban Darakta a hukumar Kimiyya da Fasaha ta jihar Katsina an yi abin da ya dace.

An ajiye kwarya a gurbinta: nada Farfesa Kabir Matazu mni a matsayin babban Darakta a hukumar Kimiyya da Fasaha ta jihar Katsina an yi abin da ya dace.

by masta

An ajiye kwarya a Gurbinta: Nada Farfesa Kabir Matazu mni a Matsayin Babban Darakta a Hukumar Kimiyya da Fasaha ta jihar Katsina an yi abin da ya dace.

Farfesa Kabir Matazu mutum ne jajirtacce mai burin ganin al’ummarsa ta farka ta nemi ilimi tare da jajircewa kan neman na kanta An haifi Farfesa Kabir Ibrahim Matazu a garinMatazu a shekarar 1966. Ya fara da makarantar allo. Ya kammala karatun firamarena a makarantar Galadima a garin Malumfashi a 1978. Ya yimakarantar sakandire a nan Garin Malumfashi ta Government Day secondary School su ne daliban farko a wannan makarantar sun kammala a 1983.Daga nan na sami shiga makarantar share fagen shiga jami’a wadda a yanzu ita ce Usmanu Danfodiyo University Sokoto daga shekarar 1984 zuwa 1987.Ya yi bautar kasa a Kano inda ya koyar a makarantar Rumfa College.Bayan ya kammala sai hukumar Science and technical ta Kano suka duba cancantata suka ba shi aiki amma saboda kishinsa ga jiharsa bai karba ba. An fara tura ni makarantar G.G.S.S Funtua a 1988 don ya koyar da chemistry shekara biyu.1990 lokacin Conel Lawan Jafaru yana Regestrer a NDA sai suka fito da tsarin yin digiri kuma ana neman malamai ‘yan arewa sai a aka dauke su aiki a matsayin kananan malaman makaranta( Asisstant Lecturer) watansa hudu a lokacin sai ya koma karo karatu digirina na biyu a Jami’ar Jos ya kammala a 1992.Daga nan sai na dawo ya ci gaba da koyarwa a NDA.A 1994 sai aka zabe shi a matsayin kansila a karamar hukumar Matazu sai kuma ya zama mataimakin shugaban karamar hukuma har sai da aka yi zabe bayan shekara biyu.Daga nan Farfesa Matazu sai na koma ya ci gaba da koyarwa har 2000. Ya koma karatun digiri na uku a jami’ar Usman Danfodiyo.Yana gaf da zai kammala karatun a 2004 Sai marigayi Malam Umaru ‘yar’aduwa a lokacin yanagwamnan Katsina ya ba shi shugabar makarantar Kimiyya da fasaha ta Hasan Usman Katsina polytechnic. Ya zauna shekara hudu. Ya maimaita zango na biyu lokacin Gwamna Alhaji Ibrahim Shehu Shema yana nan har shekarar 2009. Ya sami gurbin shiga National institute for policy and sating studies da ke Jos inda ya sami shaidar member na national Instutude MNI har zuwa 2009 ya dawo nan polytechnic har zuwa 2011.Farfesa Matzu ya zama Rector a Usaini Adamu Federal college Kazaure jihar Jigawa a shekarar 2012 inda ya shugabanci makarantar har zuwa 2015. Duk da an nemi ya maimaita amma ya nuna kin hakan. Bayan shirye-shiryen kafa jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua Farfesa Matazu ya zamo daya daga cikin ‘yan kwamitin samar da makarantar don haka bayan makarantar ta kafu aka nemi alfarmarsa kan ya dawo da aiki nan Umaru Musa inda ya zama shugana sashen Bio-chemistry daga baya ya zama Dean na faculty of natural and applied science.Farfeasa Matazu ya zama shugaban kwamitin Raktocin gaba daya na Najeriya ya rike wannan mukami shekara biyu. An tabbatar da Matazu a matsayin Farfesa a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua a sashen Biochemistry a watan Afirilun wannan shekarar ta 2023. Farfesa Kabir Matazu yana cikin ‘yan kwamitin da suka zagaya kananan hukumomin jihar Katsin don neman kur’ar al’umma kan zaben gwamna Dikko Radda.

Farfesa a Matsayin Manomi

Farfesa Matazu ya nuna noma gadarta ya yi don tun da ya taso ya tarar da iyayensa sauna noma a matsayin sana’a don haka shi ma ya gaji wannan sana’ar ta noma. Ya fara noma nasa na kansa tun lokacin da yake GSS Funtua1988 lokacin ana yayyanka fili na makaranta ana ba wa ma’aikatan makarantar. Mun yi noman tun babu riba har zuwa yanzu da darajar noman ta dawo.

Gudummawar da Farfesa Kabir Matazu ya Bayar a Ciki da Wajen Katsina

• Ya yi gine-gine a polytechnic da dama tare da kawo sababbin kwasa-kwasai.
• A Kazaure duk da ita qaramar makaranta ce amma wannan bai hana ni kawo sababbin kwasa-kwasai ba tare da yin gine-gine ta samun kwarin gwiwa da tallafin ministar ilimi ta wannan lokacin Farfesa Ruqayya.
• Farfesa Matazu yana alfahari a zaman da na yi a a Hasan Usman Katsina ya sa da yawa malaman sun koma sun karo karatu da kansa ya ke takawa ya je jami’oin ya rinka nemawa malaman makarantar guraben.
• Farfesa Matazu ya zama shugaban SUBEB da ke Abuja kuma ya sami kyakkyawar shaida a zamansa a wannan ma’aikata har zuwa lokacin da wa’adinsa ya cika. Ko a nan dinma an so ya kara zama amma shi ne ya nuna kishinsa ga jiharsa ya dawo gida inda ya cigaba da koyarwa a jami’ar jiha ta Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina.
• A zamansa na SUBEB a birnin tarayya Abuja ya bayar da gagarumar gudummawa musamman wurin inganta yanayin koyo da koyarwa da muhallin da makarantun suke ciki musamman a karkara inda wasu wuraren da kyar ake iya shiga saboda rashin tsaro da kyawawan hanya da sauransu. Amma duk da haka ya sadaukar da kansaya yi aiki lungu da sako har zuwa cikar wa’adin zamansa a nan.
• Jaridar Idon gari tana taya ka murna Allah ya yi riko da hannayenka, amin.

Related Posts

Leave a Comment