Me ake nufi da Artificial intelligence kuma menene makomar-sa?Cewar Daha Tijjani
Artificial intelligence, wata fasaha ce wadda ta ke iya kwaikwayon halayyar Dan Adam. Za a iya fassara Artificial intelligence da duk wani nau’in kwamfyuta wadda aka tsara-ta, za ta iya kwaikwayon wasu halayya na Dan Adam. A wannan zamani yanzu haka ana amfani da ita a bangarori daban-daban a masana’antu, kamar masana’antun bangaren kiwon lafiya, tallace-tallace, harkokin mulki da gudanarwa da sauransu. A wannan mukala, za mu tattauna ne akan nau’ikan fasahohi daban-daban na Artificial intelligence (Ai), da kuma yadda al’umma za su shirya don rungumar wannan sabon sauyi na fasaha domin tafiya dai-dai da zamani.
Ga yadda Artificial intelligence, ya ke.
A duk lokacin da aka tashi magana aka Artificial intelligence (AI), akan yi zantuttuka masu yawa, amma kuma ba ayin cikakken bayani (gamsashshe) da jama’a za su fahimta. Shin Artificial intelligence na nufin kawai wata na’ura ce da take kwaikwayon halayyar Dan Adam? Ko kuma wani abu ne kawai kirkirarre mai wuyar sha’ani da ake mai kallon mujiya cikin Tsuntsaye?
A wannan mukala, za mu yi kokari mu yi bayani dalla-dalla a fayyace, yadda za mu gamsar da masu sauraronmu, su fahimci me ake nufi da Artificial intelligence. Za mu duba tarihinsa da kuma makomarsa anan gaba.
Me ake nufi da Artificial intelligence?
Artificial intelligence.
Artificial intelligence, wata fasaha ce da ta ke da fadin gaske tana kuma da kananan rassa da kuma hanyoyi daban-danan. Sai dai babbar manufar wannan fasaha ita ce kirkirar wani tsari na koyo tare da sanya na’ura mai kwakwalwa ta iya kwaikwayo ko gudanar da wasu ayyuka da Dan Adam ya ke yi.
Akwai hanyoyi masu yawa da mutum zai iya kirkirar wannan tsari na Artificial intelligence.
Daya daga cikin Irin wadannan hanyoyi shine amfani da na’ura mai kwakwalwa/ inda za ka sa kwamfyuta ta koyi wasu abubuwa ko halayyar Dan Adam wato Machine learning. Idan har akwai isassun bayanai, na’ura mai kwakwalwa wato kwamfyuta tana iya gane wani tsari na fayyace abu da aka dorata akai ko hasashen wani abu da ake kyautata zaton zai faru. Wannan tsari an gwada shi sosai kuma an samu nasara, yana aiki kamar yadda ya kamata. Wannan kuma ya faru ne saboda ci gaba da aka samu wajen sabbin na’ura masu kwakwalwa da ake kerawa da kuma bayanai da aka cusawa kwamfyutocin.
Wani bangare na yadda ake amfani da Artificial intelligence shine ta hanyar wasu dalilai masu alamomi. Wannan ya kunshi shiryawa na’ura mai kwakwalwa/kwamfyuta wasu muhimman ka’idoji wanda hakan zai taimakawa kwamfyutar samun damar nadar wasu bayanai da aka riga aka cusa-su a cikin manhajar kyamfyuta. Wadannan hanyoyi sune na farko-farko kuma sun yi farin jini sosai a shekarun baya, amma a yanzu sakamakon sauyin da aka samu da kuma ci gaba a manhajar koyi da kanka, al’amura sun wuce haka.
Wasu muhimman matsaloli ne ake iya magance su ta hanyar amfani da Artificial intelligence?
Akwai muhimman matsaloli masu yawa wadanda ake amfani da Artificial intelligence wajen magance su. Daya daga cikin muhimman su shine yadda za ka sanya na’ura mai kwakwalwa/kwamfyuta ta rika yin wasu halayya ko kwaikwayon wasu halayya na Dan Adam tare da daukar mataki kan wani lamari kamar yadda Dan Adam ke yi. A zahiri wannan babbar matsala ce mai wuyar sha’ani, saboda wannan tsari na bukatar kwamfyutoci su fahimci al’amuran duniya baki daya tare da iya tuna abubuwa da suka faru a baya.
Wani muhimmin sashe na wannan fasaha na Artificial intelligence kuma shine, yadda za a iya sanya na’ura mai kwakwalwa)/kwamfyuta ta rika mu’amala da Dan Adam ta hanyar yin magana kamar yadda shi Dan Adam din ya ke yi, Ba shakka wannan yana da wahala sosai saboda akwai bukatar sanya kwamfyuta ta fahimci yarurruka/harsuna da al’adu na Dan Adam.
Daga karshe, wata muhimmiyar matsala da Artificial intelligence ke iya magance wa kuwa, ita ce, yadda za a iya sanya kwamfyuta/na’ura mai kwakwalwa ta iya kammala wasu ayyuka ko gudanar da wasu ayyuka masu dumbin yawa a lokaci guda. Wannan kuwa sun hada har da; yadda kwamfyutar za ta iya sarrafa/tuka mota ko jirgi ba tare da taimakon Dan Adam ba. Wannan kuwa babbar matsala ce mai wuyar sha’ani saboda ana bukatar na’ura mai kwakwalwa/kwamfyuta ta iya koyo cikin hanzari tare da gaggauta tuna wasu wasu muhimman abubuwa a lokacin da ta ci karo da wani sabon al’amari ko aka shiga cikin hatsari ko neman taimakon gaggawa.
Ya zan yi amfani da wannan fasaha ta Artificial Intelligence?
A rayuwar ka a wannan zamani, za ka iya amfani da fasahar Artificial intelligence ta hanyoyi masu yawa. Misali, za ka iya amfani da dabarar tsara na’ura mai kwakwalwa/kwamfyuta ta rika aiki irin na masinja ko Dan aike ko kamar yadda manhajar Amazon Alexa ko Apple’s Siri su ke yi wajen gudanar da ayyuka kamar su; sanya maka kade-kade da raye-raye don nishadinka a lokacin da kake bukata, saita maka alarm na waya don tunasar da kai wani aiki da kakeson yi nan gaba a wani lokaci, ko kuma tayar da kai daga bacci da sauransu, da kuma amsa tambayoyi. Haka zalika, za ka iya amfani da fasahar Artificial intelligence wajen yin ayyuka irin su: yin kasafi, motsa jiki don kasancewa cikin koshin lafiya ako da yaushe da kuma koyon sabbin harsuna.
A rayuwar ka, akwai hanyoyi masu yawa wadanda za ka iya amfani da fasahar Artificial intelligence. Alal misali, za ka iya amfani da fasahar Artificial intelligence ka rika mu’amala da abokan huldarka na kasuwanci ko kamfani ba tare da kai ka tattauna da su kai tsaye ba. Wannan tsari zai faru ko kana kusa ko kuma bayan ka fita. Haka kuma za ka iya amfani da hikimar tsara kwamfyuta ta rika mu’amala da abokan huldarka ta hanyar manhajar chatbots a website dinka ko a ofishinka wanda zai rika tattauna kai tsaye da abokan huldarka. Hakan zai rage maka kashe kudi sosai musamman tun da baka dauki ma’aikaci da zai yi wannan aiki ba.
Yanzu dai ina fata ka fahimci yadda wannan fasaha ke aiki tun da ai kunga hanyoyi masu yawa da mutum zai iya amfani da fasahar Artificial intelligence. Kuma fa kunsan ita fasaha kullum ci gaba ake samu, saboda haka za ku ci gaba da ganin sabbin hanyoyi nan gaba da za ku ci gajiyar fasahar Artificial intelligence.
To yanzu me za mu yi idan aka kai wani lokacin da fasahar Artificial intelligence ta kai matsayin da tafi Dan Adam basira?
Idan har aka kai lokacin da Artificial intelligence ya fi Dan Adam basira, tabbas za a ga tasirinsa cikin al’ummar-mu. Wajibi ne muyi tunani akai-akai a matsayin mu na ‘yan Adam, kan yadda muke mu’amala da kayayyakin fasaha na zamani.
Akwai abubuwa da dama da ake tsammanin za su iya faruwa idan ta kai ta kawo fasahar Artificial intelligence ta zarce basira da hikima da Dan Adam ke da su. Daya daga cikinsu kuwa shine Artificial intelligence zai zama bawan-mu inda shi za mu sanya ya rika yi mana dukkannin ayyukan da ya kamata ace mu za mu yi da kan mu. Sai dai a bangare guda Artificial intelligence zai kuma iya zama mana ubangida saboda yawan dogara da za mu yi da shi, zai sa ya zama shi ke juya-mu shine ubangidan-mu, ko kuma mafi muni shine Artificial intelligence zai iya kasancewa kishiya ga Dan Adam, yadda zai rika rayuwa kafada-da-kafada da Dan Adam, ya samar da wata al’umma wadda take da al’adarta na zamantakewar rayuwa.
Ko ma dai me ya faru, a zahiri fasahar Artificial intelligence ta kawo wani babban sauyi a zamantakewar rayuwar bil’adama. Dole ne mu saba da rayuwa a duniyar da na’urar zamani za ta fi Dan Adam basira da hikima. Tabbas babban kalubale ne, wanda dole mu tashi tsaye domin tunkararsa.
Gaskiya Tafi Kwabo


1 comment
Good