MALAMAI MAGADA ANNABAWA
Daga
Bilkisu Yusuf Ali
Tarihin rayuwa Sheikh Abdullahi Dandume
Nasabarsa
Sheikh Abdullahi Dandume Dan Yaqub Dan Ibrahim Dan Abubakar nasabarsa tana danganawa har zuwa wali Danmasani wannan babban waliyyi da ka taba yi a qasar Katsina. Mahaifin sheikh Abdullahi Liman Yaqub ya baro garin Katsina na wancan lokacin daga ya koma Kwatangiri sakamakon mu’amalar ‘ya’yansa da Turawa sai ya koma Dan’maiyaqi wanda daga bisani dalilin yada ilimin addinin muslunci ya koma qasarsa ta haihuwa a wannan gari ne aka haifi sheikh Abullahi Dandume. An haife ahi a Shekarar 1916 Kuruciyarsa
Sheikh Abdullahi ya tashi da kyakkyawar quruciya sakamakon tarbiyya da ya samu ta iyaye da kuma sufanci ya kuma samu tarbiyyar islama don haka tun tasowarsa ya tashi da haquri da jiuriya da son karatun alqur’ani da sauran fannoni. Neman iliminsa
Sheikh Abdullahi Dandume ya fara neman ilimi ne a gaban mahaifinsa Sheikh Liman Yaqub tun daga matakin karatun alqur’ani mai girma sannan ya karanta littattafan fiqhu kamar qawa’idi zuwa risala duk a gaban mahaifinsa daga nan sai ya fito zuwa Tsaure inda ya goge a Bangaren qur’ani da sauran da sauran littattafai na hukunce-hukunce. Ya zauna a Zariya gidan Malam Na’iya inda anan ma ya tumbatsa a fannoni daban-daban na addini. Har wa yau ya zauna gidan sheikh Abdullahi Yahuza a nan dai garin zariyan ya kuma zauna a garin Kano duk dai neman ilimi. Abokan Karatunsa
Daga cikin abokan karatunsa akwai:_
Sheikh Balarabe Gusau da Sheikh Ja’afaru Katsina da sheikh Iliyasu Garo da Sheikh Abduqadir Zariya. Malamansa
Malamansa sun haDa da Malam Na’iyya Zariya da sheikh Yahuza Zariya da Ma’aji Ishaqa da Sheikh Abdullahi Salga da Sheikh M. Mijinyawa Almajiransa
Kasancewa Sheikh Abdullahi Dandume mutum ne mai tarin ilimin addinin muslunci kuma shehun Tijjaniya dan fairar sheikh Ibrahim Inyass (RTA) Sheikh Abdullahi yana da almajirai da muridai da daman gaske sai dai a kawo kadan daga cikinsu. Daga ciki akwai:-
Sheikh Ibrahim Hunquyi da Sheikh Khadi Dandume da Sheikh Ibrahim Babba da Sheikh Ibrahim Mai ayaba da Sheikh Ibrahim na Qanqara da Sheikh Qasim mai unguwar Sallah da Sheikh Muhammadu Kurna Kano da Sheikh Malam Adamu Katibi Kano da Sheikh Inuwa Damari. Halayensa
Sheikh Abdullahi Dandume ya kasance mutum mai haquri da jama’a , ba ya da fushi a kowanne yanayi yakan danne vacin rai musamman ma idan shi aka tava yakan nuna wannan abin ba komai ba ne. Tarihi ya nuna Sheikh Abdullahi ya sa wahala wajen magabata masu wauta daban-daban . Kuma yakan hana magoya bayansa xaukar mataki akan duk wanda ya kawo masa wauta ko da kuwa ya cutar da shi duk kuwa da tarin almajirai da magoya baya da yake da shi.
Sheikh Abdullahi mutum ne mai tausayi da jin qai sannan ya kasance mai taushin zuciya babban abiin da ya fi qauna shi ne ya ga ya gina Dan’adam wannan ta sa yake da Allah ya yi masa gaggarumar baiwa ta fuskar tafiyar da jama’a. Mutum ne mai tsantsar gudun duniya da juya mata baya. Kyauta tana cikin halayensa da sa Boyuwa ba yadda za a yi a zo wajensa bai ayar da kudi ba ko kuma bai bayar da rigunan sawa.
In kuwa na zo batun ibada Sheikh Abdullahi mutane sun yi masa kyakkyawar shaida a tsahon shekara arba’in ba su ga lokacin da salla a cikin jam’I ta wuce shi ba. Tafiye- Tafiye
Sheikh Abdullahi Dandume mutum ne mai sha’awar tafiye-tafiye ciki da wajen qasar nan ya ziyarci qasa mai tsarki (Makka) don yin hajj da umara kuma ya ziyarci madinatu Fas ya kuma yi dabdala zuwa madinatu Kaulaha da ke qasar Senegal domin ziyartar sheikh Ibrahim Inyas. Ya ziyarci qasashe irin su Niger da Chadi da qasashe da dama a yammacin Afrika. A cikin qasar Najeriya kuwa ba inda bai taka ba indai garin akwai wata zawiyya ta Ahlillahi. Duk inda ka zaga zaka iske labarinsa da ziyarar da ya kawo. Rasuwarsa
Sheikh Abdullahi Dandume ya rasu Ranar 25/Rabiul Auwal 1410 na Hijra Wanda ya yi dai-dai da 24 ga watan Oktoba 1989. Allah ya jikansa da gafara Amin.
An Sami Wani sashen wannan tarihi daga jikan Sheikh Abdullahi Dandume Sheikh Rayyahi

