Home Labarai Kamar Kwankwaso bai Hankalta ba

Kamar Kwankwaso bai Hankalta ba

by masta

Ali Abubakar Sadiq
aleesadeeq1@yahoo.com
08039702951

Kwankwaso na daya daga cikin mutane biyu da suka sa na hankalta da yan siyasa, yadda na daina so ko kin duk wani dan siyasa, na zama sai dai na na so halin kirki na dan siyasa ko kuma na nuna kiyayya ta ga mummunan halinsa. Bayan dawo-dawo a shekara ta 2011, cikin shekaru biyu kacal, Kwankwaso ya dagula tunaninmu ganin yadda ya bijiro da manya-manyan ayyuka musamman gadojin sama da tun lokacin Shagari aka yi ta burin ganinsu a Kano. Ya farfado da baiwa dalibai tallafin karo karatu a kasashen waje, abinda tun gwamnati Rimi ba a sake yi ba. Ya gina dubban azuzuwan makarantun firamare tare da sabbin makarantu (irinsu governor college). Ya samar da sabbin makarantu na sana’o’i sama da goma. A takaice dai Kwankwaso ya tonawa duk wani gwamna a Arewa asiri, domin ya nuna cewa matukar akwai nufi, to gwamnati na da kudin da zata aiwatar da manyan ayyuka na raya kasa.

Wannan dalili ya sa a shekarar 2013, na rubutawa gwamna Kwankwaso shawarar ina bukatar ya bani dama domin na tattara manyan ayyukansa a littafi domin ajiye tarihi da kuma baiwa magadansa damar kwaikwayo. A lokacin na sadu da shugaban harkokin yada labarai na gwamna Dantiye, na bashi tsarin, wanda karara ya kukkushe aiki na da nuna cewa ai suna da ire-iren aikin fiye da nawa, kamar dai yana hassada. A karshe dai bayan Allah ya sa takardar tawa ta isa gaban Kwankwaso da taimakon mai daukar hotonsa, Ali Indabawa, nan take Gwamna ya sahale da na ci gaba da aiki, kuma ya bada umarni ga Daraktan Bincike da tattara bayanai na gidan gwamnati da su bani duk wani hadin kai da takardu da zan bukata. Na kama aiki gadan-gadan ba tare da an bani ko sisin kwabo ba, na karade gari daukar hotunan ayyukan tare da ziyartar manya ofisoshin gwamnati domin karbar bayanai. Na gamu da cikas da hassada iri-iri daga manyan ma’aikata maza da mata. Wata Darekta ma a SUBEB karara ta ce min, zan yi aiki na sami kudi suna zaune! Ku ji fa?

Haka-dai haka-dai cikin kalubale na samu na kammala aikin sannan na mayarwa wancan hukuma da aka hada ni da ita littafin domin nazari su tabbatar da cewa na yi aikina daidai. Akwai wata ma’aikaciya a gidan gwamnati wadda mun taba halartar wata bita da gwamnatin Amurka ta shirya mana a Abuja, mun kwana 7 a hotel daya muna bitar, amma sai ta nuna bata taba ganina ba sakamakon wannan aiki. Bayan nan sai aka turawa gwamna wanda ya sahale da a buga littafin na Hausa da Turanci, amma dai sai suka sayi kwafi 1000 na Hausa suka barni da na turancin ba su siya ba. Shin ba’a zalunce ni ba? A sa ni na yi aiki a ki siya? Dalilin baku wannan labari domin gane yadda hassada ta mamaye al’ummar hausawa a yau.

Bayan na kammala littafin ina nazari, sai na lura cewa babu wani bangare da Kwankwaso bai taba ba a wannan lokaci idan banda harkar karfafawa da samar da jari a harkokin noma, duk da dai ya farfado da kamfanin takin zamani na jiha. Wannan abu da na lura da shi ya sa na nemi wani mai bashi shawara da a roke shi da ya saka ko da biliyan biyar a bangaren noma kafin ya kammala mulkinsa. Abin mamaki wannan mai bada shawara ya ce amsar da Kwankwaso ya bayar shine “Idan ka saka kudi a noma wanene zai gani?” Wannan bayani ya tayar min da hankali kuma ya nuna cewa yan siyasa bukatar su ce a gaba ba al’umma ba, abinda ya sa na sake nazarin duk ayyukan da gwamna yayi a wannan dan tsukukun.

Na lura cewa duk gine-ginen azuzuwa masu bene sama da 800 sababbi da gwamna ya gina, baya ga rashin samar da tsarin kujeru da tebura, kashi 90 zaka ga an gina su a bakin hanya ne an yi watsi da wadanda ke cikin lunguna (wato dai sai a inda za a iya gani kenan ko?). Makarantu sama da goma na sana’o’i ba a yi tsarin yadda zasu rayu bayan gina su ba, yadda da dama dole aka maida su wani abu, ko kuma su na nan a yashe sai kangon ginin. Kwankwaso ya debi biliyoyin kudaden yan fansho ya gina katafarun biranen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo wadanda idan banda Abuja duk fadin Najeriya babu irinsu. Amma su ma babu tsarin dorewarsu, yadda bayan kusan shekaru goma akasarinsu na nan a yashe, kuma Ganduje da ya gaje shi shima yayi biris da wajen yadda akwai gidajen da aka balle kofofinsu da wasu kayayyaki. Wannan kadara da a ce ta Kwankwaso ko Ganduje ce, don Allah zasu wofintar da su haka? Baya ga jefa yan fansho cikin masifu da daukar kudaden su ya yi. Makarantun Kano mafi alfahari na Science da ke Dawakin Tofa da Dawakin kudu, sun durkushe sakamakon gwamnatin Kwankwaso ta samar musu da kishiyoyi irinsu Jan Baki, Governors College da First Lady wadanda a yanzu ko ita Governors College din an daina jin duriyarta.

A karshe dai ni abinda bincike da nazari na ya nuna min shine cewa duk wadannan ayyuka da Kwankwaso ya bijiro da su a wancan lokaci dalili ne na kashin kansa ba don al’ummar Kano ba, wato yayi wadancan ayyuka ne kawai domin cimma burinsa na samun takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC. Kuma anga tasirin haka yayin da ya buge Atiku ya zama na biyu a bayan Buhari wajen tsayar da Dan Takara a 2011. Amma kuma sai gashi ya shafe shekaru takwas bai sami wani mukami a cikin gwamnati ba.

Kowa ya ga yadda a ka yi murdiya a zaben 2019 kuma duk mai kishin Kano na hakika abin yayi masa zafi. Allah cikin hikimarsa sai ga shi a 2023 nasarar da aka kwacewa Abba ta dawo kuma Kwankwaso ya murkushe duk wani dan siyasa a Kano a 2023. Wannan gagarumar nasara da Kwankwaso da Abba suka samu, ni’ima ce daga Allah da sakamakon zaluncin da aka yi wa Kanawa a 2019. Kwana guda bayan Abba ya ci zabe na yi rubutun taya shi murna da tunatar da shi cewa a yanzu kuma “Kanawa ne ke binsa bashi” kuma abinda ke gabansa shine biyawa Kanawa bashi wajen lalubo hanyoyi da zai kyautata rayuwarsu, amma abin takaici Abba ya share wata guda ba abinda ya saka a gaba banda rushe-rushe, abinda ya nuna karara cewa bai yiwa Allah shukura ta samun wannan kujera ba ballantana ya fara biyan kanawa bashi. Tun kafin a rantsar da shi, kungiyar mu ta NDF mai kishin ci gaban Kano ta saka mu a kwamiti da zai yiwa Abba murna, tare da bashi shawara game da kalubalen da zai fuskanta. Takardarmu ta isa gare shi ta sakon taya murna da neman izinin ganinsa mu isar da shawarwarinmu a rubuce (a kyauta) wadanda nazari ne da binciken masana yadda Kano zata iya samar da biliyoyin daloli na kudaden shiga kuma ya bata damar aiwatar da ayyuka. Har zuwa yau bamu sami amsar yiwuwar ganinsa ba. Kano na da kalubale musamman idan muka yi la’akari da yadda hatta Kaduna a yau ta yi mana fintinkau a kan kudaden shiga da take samarwa, kuma dan abinda gwamnatin tarayya take samarwa da an biya kudaden albashin ma’aikata na jiha (kimanin biliyan 6) da na kananan hukumomi (biliyan 3) jumlatan wajen biliyan 9 kenan sai kaga ba wani abin azo a gani don ayyukan raya kasa. A baya ma sai gwamnatin ta hada da bashin banki take iya biyan albashi idan kaso daga sama ya yi kasa. Ya ilahi yaya jiha kamar Kano mai dimbin albarkatun ruwa, na kasar noma da yawan jama’a zata zama kamar almajira sai karshen wata ta mika kokon bara a watsa mata tsaba?. Babban kalubalen da ke fuskantar Kano a yanzu shine maganar tattalin arziki da tsaro, wadanda ke tafiya tare. Gwamnati ba abinda ya kamata ta sa a gabanta irin yadda za ta fadada tunaninta wajen lalubo sabbin hanyoyi (ba na haraji ba kawai) da zasu samarwa jihar kudaden shiga da ayyukan yi ga matasan da suka jajirce wajen kawota, sannan ita kanta ta iya gudanar da ayyuka masu amfani. Amma kash! Maimakon hakan sai ga gwamnatin ta bige da ta’azzara yanayin tattalin arzikin jihar ta hanyar durkusar da wasu masu sana’o’i da ke samarwa daruruwan mutane ayyuka ta hanyar rushe-rushe. Idan da an maida hankali wajen rushe gine-gine da ke cikin makarantu, masallatai, makabartu da lambuna ai babu laifi. A yau babu wani lambu a birnin Kano, amma ana rushe wurare irin cikin Daula ko gidajen mai da da shaguna da ke titin BUK wadanda ke da tasiri na habaka tattalin arziki da samar da aikin yi.

Kada mu manta gwamnatin Kwankwaso, daga 1999-2003 ita ta fara yanka filayen shaguna. Bamu manta yadda gwamnatin tayi ta kai ruwa rana da jami’ar Bayero ba, sakamakon yanka filaye a jikin katangar jami’ar da ke kan Gwarzo road, da yanka fadalar da ke daura da kofar shiga BUK da jikin FCE da kuma na gidajen gwamnati da ke kan hanyar Kabuga zuwa Tal’udu. Ina adalci da zaka ce a rushe daga Dan Agundi zuwa kofar famfo amma a bar daga kofar famfo zuwa kabuga? Ko ka tsallaka garin Bichi?
A baya Kwankwaso ya rushe ginin Amaryawa a farm center a karon mulkinsa na biyu, dalilin cewa yana kusa da hanyar ruwa. Amma kuma daga baya ya baiwa masu sana’ar waya damar yin shaguna a kan kwatar ita kanta. Kuma mai ginin ya shiga kotu neman hakkinsa wanda a lokacin Ganduje a ka yi sasanci a wajen kotu kuma gwamnati ta biya daruruwan miliyoyi na diyyar rushe masa gini. A wancan lokaci babu wani gini da ke da studio da na’urori na harkar media kamarsa a Kano. Wa aka yiwa asara idan ba kanawa ba?

Kwankwaso ya janyowa Kanawa asarori irin wadannan, kamar filin K/Na’isa, makarantun sana’o’i, kwankwasiyya, Amana da Bandirawo. Amma laifin ba na Kwankwaso kadai ba ne, Kano ta rasa manya, da alama sai manyan wukari, kamar yadda Baba Ganduje ya taba fada kenan ko? Akwai alamun gaskiya a zancen Ganduje domin Malamai su ya kamata su zama idanuwan al’umma, amma mun wayi gari a maganar Gandollar video sai ga shugaban Izala, Saleh Pakistan, ya jagoranci tawagar Malamai zuwa mubayi’a ga Ganduje, kuma a kokarin tumasanci har da kwatanta cewa yadda Allah ya wanke Nana Aisha daga zargin Zina haka suke tsammani Allah zai wanke Ganduje daga badakalar dollar? Subhanallah. A Kano mun ga yadda na gindin Sarauta suka hada baki aka rushe karfi da ikon masarauta. Mun ga jerin sunayen hamshakan attajirai ana yanka filin jama’a ana basu. Manyan yan siyasa kamar jemagu, yau su na makale anan gobe su koma can sababin kasuwar bukata. Rashin manya na hakika, shi yasa Ganduje ya ci karensa babu babbaka, ga Abba ya dora.

Hakika kowa ya ga irin barna, hadama da handama, rashin sanin ya kamata rashin kunya na gwamnatin Ganduje, amma kowa kuma ya san barna ba za ta taba gyara barna ba. Ya fito fili karara cewa kwankwasawa sun shigo mulki a fusace tare da kullacin ramuwa. Hakan kuskure ne babba a mulki domin shi shugaba uba ne, kuma shugaba wajibi ne yayi adalci ga kowa domin shi adalci wajibi ne a kan masoyi ko makiyi. Kuma an ce da na gaba ake gane zurfin ruwa. Kwana guda tal daga saukar Ganduje kowa yaga irin wulakantar da shi da Gwaggo suka fuskanta a wajen rantsar da Tinubu. Wannan ya ishi duk wani mai mulki ya gane cewa babu abu mai dorewa face aiki tsakani da Allah. Don haka muna sake kira ga Kwankwaso da Abba da su dubi girman Allah su ajiye wannan gaba a gefe su yi mana aikin da muka zabe su. Kada su manta kuma cewa Kano ta yi musu riga da yar ciki har da malun-malun ta halarci, sakamakon zabensu sau biyu-biyu. Wallahi Kanawa ke binsu bashi.

A karshe, kira na ga Kwankwaso shine ya kamata ya hankalta da yadda wayonsa bai bashi takara a 2011 ba, kuma yayi azumin shekara 8, amma Allah ya sake bashi dama a yanzu, wallahi ya ji tsoron Allah ya cire gaba ya yi adalci wajen saka Gwamna ya yi abinda ya dace cikin adalci. Kuma shekara hudu kamar yau ce, kuma Kano ta san na ki. Sannna ina kira ga mutanen Kano su gane cewa yan siyasa a kullum na amfani da mu domin cimma wata manufa ta su, matukar muna son su amfane mu, sai mun daina makauniyar siyasa, mu rika son duk wani dan siyasa a sakamakon alherinsa idan kuma ya zo da akasin haka mu nuna kiyayyar mu ga haka. Ta haka kadai yan siyasa za su rika yi mana ayyukan da muke bukata ba ayyukan da su ke so ba. Allah ya agaje mu gaba daya.

Related Posts

Leave a Comment