Lafiyar IyaliTare da
Bilkisu Yusuf Ali
Yadda mace za ta kula da kanta bayan ta haihu
Bayan mace ta haihu yana da kyau ta kula da kantakwarai da gaske don maye gurbin raunin da ta yi tunDaga daukar ciki da wahalhalun laulayi zuwa girmancikin da dawainiyar nakuda zuwa haihuwar. Mata da yawa bayan haihuwar fari mazansu kan yi ta korafi kanwasu sauye-sauye da suke gani daga bangaren matanwanda kuma da dama daga wannan sauyin rashin gyarane bayan haihuwa da rashin tuntubar masana kiwonlafiya ke janyowa. Mata kan fuskanci rashin ni’ima kobushewa ko karuwa ko ftar wari ko zubar ruwa da daisauran matsaloli. Akwai abubuwa da dama da mace yakamata ta mayar da hankali a kansu tun lokacin da take da ciki kama daga abinci da motsa jiki da kulawa da kai da sauransu wanda tun daga lokacin ya kamata a fara tattalin al’amuran da za su biyo baya bayan an haihu.
Bayan mace ta haihU tana bukatar :-
• A ke shiga ruwan zafi mai tsafta wanda aka sakawa ganyen magarya da gishiri kadan na dan lokaci.
• Kama ruwa da aka tafasa da Bagaruwa da lalla a yitsarki da shi sau uku a rana.Iya kama ruwa kawaiba wai ki cusa lallai a gaba ba.
• Akwai dahuwar kaza ta musamman da ake yi da itatuwa da ganyayyaki don mai jego.
• Yin salala da garin Hulba a kalla sau daya a rana.
• Shan zuma mai kyau kullum babban cokali a kallasau uku a rana.
• Cin kyakkyawan abinci mai inganci da gina jiki.
• A ci abinci a `koshi ban da zama da yunwa
• Ban da cin fara da mai in kuwa za a ci to a tabbataran sa mata ko da kifi ne ko nama ko kwai da ganyedon ingantata.
• A kalla nama ko da ba yawa musamman gashi basoyayye ba ko kuma a yi farfesu. Ya danganta da arzikin mutum, Amma dai shan romo yana da muhimmanci.
• Ya kamata mai jego ta sani tattalin abinci ya fi muhimmanci fiye da tattalin kayan da za a sakaranar suna da kuma abin da za a tara mutane su ci.
• Kula da gashi ko a tsugunna a garwashi da aka tabbatar da tsaftarsa ko ruwan zafi me tsafta(amma bisa yadda likitoci suka shar’antamusamman idan mace ta samu kari a yayinhaihuwa.
• Yana da kyau a nemi shawarar masana lafiya kankari da mace ke samu a matuncinta yayin haihuwa. Sau tari mace kan haihu a gida kuma ta samu kariba ta tare da ta sani ba. Shi ma irin wannanmatsalolin kan janyo rashin jituwa da maigida.
• Tsafta tana da muhimmanci kwarai da gaske maishayarwa tana yin karni saboda nono da take bayarwa don haka mata su kiyaye sa turare a jikinsu. Amma kuma ba yadda zai cutar da jaririba.
• Shan magunguna da kan kara ni’ima musammankayan marmari da madara shi ma zai taimakakwarai da gaske saboda mayar da abin da aka rasa da gajiya da wahalhalun daukar ciki. 

