Home Labarai In Budurwarka ta ishe ka da ba -ni-ba-ni ka fece, ba matar aure ce ba! Kwarya ta Gari na ragaya

In Budurwarka ta ishe ka da ba -ni-ba-ni ka fece, ba matar aure ce ba! Kwarya ta Gari na ragaya

by masta

Zamantakewar Iyali

Tare da

Bilkisu Yusuf Ali

Ya zan zabi mace ta gari

Babbar hujjar da yawan mata kan rike na kallon mazamayaudara ne shi ne na kin aurensu duk kuwa da soyayyar da suka sha amma a karshe sai ka ji sun cewai suna neman mace ta gari. Bahaushe kan ce waikwarya ta gari na ragaya. Maza sukan zama a rude yayin da suka tashi neman mace ta gari har sukan shigashakka kan wace ce macen da ya dace su aura amsar da suke samu ita ce su yi duk inda za su yi su lalubi maikamun kai daga ita ne ake samun mace ta gari.Ita kuwamai kamun kai siffofinta a bayyane yake inda namiji in ka qura ido ka tsanannta nema to za a dace.

Mace ta gari ita macen da Bahaushe ke kira mai kamunkai wadda ta siffantu da kakkyawar dabi’a da halaye da kamala kallo daya za a iya gane tarbiyyarta da qoqarinda iyayenta suka yi wajen ba ta tarbiyya. Mace ta kwarai ita ce wadda kowanne namiji mai hankali zai yifatan a ce tana gidansa ta zame masa sanyin idaniya ta zama al-mar’atissaliha da Annabi Muhammad (SAW) y ace ta fi duniya da duk abin da yake cikinta.Maceingantacciya ita ce dai matar da kowanne namiji zai so ya sami zuriya da ita.

Mata da dama da za ka tattauna da su shi ne babbarmatsalarsu mijin aure abin haushi da ke damunsu gamasoyan nan kamar jamfa a Jos amma auren yagagara.Mata na ta wahala addu’a da ‘yan dabaru du kana ta fama amma abu ya qi yi wuwa.Tashin hankalinba ga matan ba zawarawan ba.Mace wadda ba ta da makusa ta kowanne bangare kyau ko asali ko ilimiamma aure ya gagara ana ta laluben dalili an kasa ganogaskiya abu guda ke zagayawa a kwakwalwarsu shi ne maza mayaudara ne amma fa duk yaudararsu sunaneman mace ta gari ne don sa wa a daki.

Kamun kai

In ka tashi neman matar da za ka aura ka dage ka nemimai kamun kai . Yana cikin matakin farko da mace yakamata ta fara nunawa a gun duk wanda take so suqulla mu’amala da ta take fatan dorewarta zuwa aure.Hanyoyi da dama za ka lura da shi in kana son ganemace mai kamun kai kada ka jira a b aka labari kai da kanka za ka sa ido ka lura. Mata a yau a tunaninsuyadda suke ganin maza na haba-haba da mata ba tare da nuna wani zave ba to su sani iyakar ta waje ne.

Sutura

Sutura ita ce abin da ake sanya a jiki don kare tsiraici.A sutura ana gane kamalar mutum. Abu na farko da kan ja hankalin namiji ga mace har ya gane ajin da zaiajiye ta shi ne irin suturar da ta saka jikinta

Mata a yau suna tunanin bayyana tsiraicinsu shi ne hanyar da za su iya janyo hankalin namiji gare su harya gane kyan wani bangare na jikinsu da zai kai su gaaure. Wannan kuskure ne namjin da wannan zai daukihankalinsa har ya yi tunanin ku yi sabo to tabbas saidai soyayya wanda a qarshe da-na-sani ne zai biyobayan haduwar. Yana da kyau mace ta yarda da cewamijinta duk inda yake zai tarar da ita sannan ba wanidace da za a samu a sabon Allah.

Surutu

Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai macenkwarai ba a santa da xaga harshe ba ko da a cikin‘yan’uwanta mata ne bare kuma maza.Wata matar tanatunanin in ta shiga dandazon maza ta daga muryarta da zaqewa shi ne zai janyo hankalin namiji kan su. Mace mai surutu rau-rau a kan titi ko cikin maza ba ta cikinirin matar da ka ke nema ka aura.

Mace mai kamewa da qarancin Magana ko da kuwa a wajen saurayin ne abar yabo ce da soyuwa ko da batunauren ne irin su ake nema a adana a gida

Kunya

Bahaushe ya ce kunya marin da. Ka tabbatar matar da z aka aura mai kunya ce don kuwa duk macen ta gari an santa da kunya da yakana da kara mace ba ta isa mace abin sha’awa in har ta zamanto fitsararriya. Akwaihanyoyi da dama da mace za ta nuna kunya.

• Ciye-ciye

Mata a yau sun zubar da kyakkawar al’adar nan ta kame kai wajen ciye-ciye a kan hanya ko gaban samari.Mace mai ciye-ciye da rashin kimtsi ko ga sa’anninta mata ba ta farin jini bare maza. Duk matar da ka gantatana ciye ciye kan turba bar ta kawai ba ta shiryasamun mijin aure ba.

• Roko

Roqo shi ma wata hanya ce ta nuna rashin kunya da mata kan dauka hanya wayewa.Duk matar da ta fiyeroko tana kashe wa kanta wata daraja ne ga mai sontakuma in har mace ta fiye roko to fa tana nunawawannan da zai aure ta irin zaman da za su yi. Hali nafarko da za su sa a ran su in har suka kai ki gidansu baza ki iya hakuri da samu da rashi ba sannan duk randababu ba za ki iya rufa wa zamantakewar asiri ba.Roqoga mace babbar hanya ce ta zubar da mutunci. Don haka in budurwarka ta ishe ka da ba-ni-ba-ni na bagaira ba dalili to fita a guje ba ba matar aure ce ba.

• Kallo

A kallo kadai ana iya bayyana halin mace tarbiyyartada kunyarta da dacewa ka kai ta gida ko kuma ba za kakai ta ba. Ka lura da yadda wadda za ka aura take kafeka da ido ba rusanawa to ka bi a sannu.

Rashin jan aji

Mace ta kirki da jan aji da kamewa aka santa. Ba wai ta zama mai girman kai ba amma ka nemi wanda ta san darajar kanta. In har mace za ta zama arha kowannenamiji ya kira ta ba tantancewa ta je, kowa yakebukatar jin hira ko yawo ita za a zo nema a tafi da an ceana sonta to fa kasuwa ta bude ba sauran excuse to famai irin wannan halin tza ta jima wurin neman mijinaure . Kai ma me neman matar kwarai kada ka leka.

Zafin soyayya

Anan ba sai na yi dogon sharhi ba ku maza ku ne ku kelallavawa ku nemi yarinya da buqata ta biya ba kwakuma komawa mu a vangarenmu mata sai mu ce rashinalqawari ne ya janyo haka amma ku kuka san dalili don haka ni a nan ba ni da ta cewa. A wannan gabar yaragewa matan tunda sai me karfin rabo saurayi keneman mace a qarshe ya aure ta.Na san zai yi wuya kona ba ka shawarar idan haka ta afku duk da ba a fata nace ka aure ta ko na fada ba ji za ka yi ba.

Abin nufi dai da wannan rubutu shi ne qwarya ta garina rataya. Maza irin wannan suke nema su kai gida. Qalubale ne ga iyaye su sa ido kan tarbiyyar ‘ya’yansusannan su ke nusar da su abubuwan da ya dace natarbiyya.

Allah ya sa mu dace amin.

Related Posts

Leave a Comment