Home Labarai Alh Musa Dankwairo Muradun Tarihinsa da gwagwarmayar waka

Alh Musa Dankwairo Muradun Tarihinsa da gwagwarmayar waka

by masta

ADABI MUDUBIN RAYUWA

Tare da

Bilkisu Yusuf Ali

Alhaji Musa Dankwairo Muradun

Makada Alhaji Dankwairo Muradin ya bayar da gagarumar gudummawa wajen gina adabin Hausawa.

Wane Makada Musa Dankwairo?

Marigayi Alhaji Musa Dankwairo Muradun an haifeshi a shekarar 1902 a wani gari da ake kira Dankaduda ke cikin masarautar Bakura a jaharZamfara.Mahaifinsa shi ne Makada Usman Dankwanagga Lokacin da Alhaji Musa Dankwairo yakai shekara biyar da haihuwa sai soyayya da qullutsakanin mahaifin Alhaji Musa Dankwairo da SarkinMuradun Ibrahima na Daya. Wanda suke kira sarkinKaya Iron Na Daya. Wannan soyayyar ce ta janyocirewa gaba Daya ta Usman Dankwanigga daga garinDankadau zuwa Muradan wajen wannan basarake A shekarar 1905 . Lokacin marigayi Musa Dankwairoyana Dan shekara biyar da haihuwa nan suka ci gabada sha’anin waka amma ta fada da shi da yayyanshi irin su Audu Kurna da sauransu. Haka dai ya yi ta yiwa sarkin qaya Ibrahimu waqa har wani lokaci da yatafi Makka lokacin ana zuwa Hajji a qafa ko bayan da ya dawo sai ya daina waqa ya miqa ragamar kida gadansa makdai Audu Kurna yayan Alhaji Musa Dankwairo sai Musa Dankwairo

Yaushe Alhaji Musa Dankwairo ya Fara Kida

Lokacin da Audu Kurna ya fara jagorantar kida shi maya ci gaba da amshi lokacin da ya fara girma sai ya faranasa kidan amma na noma. Amma ci gaba da bin yayansa yana amshi a kixan fada yana bin Audu Kurnakixan noma yana fita da ganga yana bin manoma.Yanadaukar tawagar ‘ya’yansa irin su Garba da Mammandan makaxa ya tafi da su qauyuka suna noma. Yayikixin da dama anan qasar Muradun din ya yi a qasarTsafe da sauran wurare da dama .Misalin kidin nomaakwai wadda ya yi wa Kogon ‘Yankuzo hakimin‘Yankuzo a qasar Tsafe inda yake cewa

: Masu gari suna noma

: Zuciya tai tana gona Maamman

: tsabe yake da noma

Akwai wadda yake cewa

: Ya riga su gona

: Mai kalmin wuce maza

Akwai ta

: Gajin mamman tawaye

: Yana gona bai gaji ba

Da ire-iren waxannan kuma duk da ganga ya yi su .Saidai daga baya ya sabunta su da kotso.

Ta Yaya ya Samu Laqabin Dankwairo?

Ya samo laqabin Dankwairo ne a lokacin akwai waniyaron mahaifinsa ne wanda suke amshi tare yana da wata ‘yar murya muryar sai ta yi kama da ta Musa Dankwairo shi wannan mutumin an ace masa Kwairosai ake cewa kamar Dan Kwairo wannan shi ne dalilinlaqabinsa.

Shaharar Dankwairo

Bayan mahaifinsu ya bar waqa yayansa ya daukigabacin gidan ana ci gaba da kidi ana kidin fada da Maradun da Sokoto da sauran wurare a 1957 saimarigayi Firimiyan arewa Sir Ahmadu Bello ya zokamfen na jam’iyyarsu Salama NPC Jam’iyyarmutanen arewa to an ce akwai al’adar da ake yi dukinda ya je akwai makadin wannan waje yana hawa yayi masa waqa sai aka sami akasi shi Audu Kurnashugaban tawagar baya nan wasu sun ce ba shi da lafiya ne a lokacin wasu kuma sun ce waje wani qauyene gun wata hidima. To ga sardauna ya sauka Maradunga Audu Kurna baya nan don haka aka tilasta a nemoqaninsa ya yi kidi saboda tasirin mawaqa da siyasa. Anan ya yi masa waqar

: Kada mara ke giwa ba a haye ma barde

: Amadu dan Ibrahimu bai yada gudun arna ba.

Duk da manazarta suna ganin wannan waqar duk da xan siyasa ya yi wa waqar ta fi kusa da waqar fada don a ciki yana cewa jikan mujaddadi jikan AbdullahinGwandu ana ganin ta wuce waqar siyasa.

Su Wa Ya Yi Wa Waqa

A shekar 1960 aka nada hakimin Muradun wato Sarkinqayan Muradun marigayi Muhammadu Tambari ranadaya aka nada shi da marigayi ‘yan doton Tsahe AliyuAllah ya jiqansu da rahma Amin.Da suka baro fadarmai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Abubakar 3 sunzoinda za su yi bankwana sai shi ‘Yandoton Tsafe ya roqialfarmar sarkin Kaya ya ba shi aron Audu Kurna ya zoTsafe ya yi masa waqoqi sai shi sarkin Kayan muradunya ce a’a amma ga dai qaninsa nan Musa Dankwairo yabi ka ko shi ba din-din-din ba y zo in lokaci ya yi yadawo wajenmu ya ci gaba da sha’ani. Wannan shi ne farkon kidin fada ga shi Alhaji Musa Xankwairo.Shi ne waqar da yake cewa :-

: Mai wuyar gaba ya hana wargi ‘Yandoto

:Bi da arna bai yarda a kai mai wargi ba

…ciki har yana faxin naxa ni sarkin kixi na jekada saimu ta duniya

Kurna na ga Sarkin Kaya Kwairo makaxin ‘Yandoto

Marigayi Alhaji Musa Xankwairo ya rasu a shekarar1991. Allah ya jiqansa da gafara amin . MarigayiDankwairo ya sami magada. Garba shi ne Dankwairona biyu sai kuma Chiroma Garba, sai yanzu Danjumawanda yake riqe da Halifancin wannan gida.

Tattaunawa da Hon Alhaji Ibrahim Muhammad Xanmadamin Birnin magaji Kuma kwamishinan kudida kasafi na jihar Zamfara. An yi hirar ne gidan RadiyoNajeriya Kaduna a filin kundin mawaqan Hausa tare da muhammad Sayaya.A shekarar 2018

Related Posts

Leave a Comment