Home Labarai Dr Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible ) ya ba wa gwamnan Kano Abba Shawara kan yadda za a binciko filayen da gwamnatin Ganduje ta yi kasafinsu

Dr Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible ) ya ba wa gwamnan Kano Abba Shawara kan yadda za a binciko filayen da gwamnatin Ganduje ta yi kasafinsu

by masta


Tsohon Kwamishinan addinai na gwamnatin tsohon gwamna Ganduje wato Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya shawarci gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf da ya kafa wata hukuma da zata duba yadda akayi tasarrufi da filayen gwamnati daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Cikin wata tattaunawa da yayi da ƴan jaridu a Kano, ya ce hanya mafi sauki da za a gano irin ɓarnar da gwamnatin da ta gabata tayi akan harkokin filayen shine kafa wancan kwamiti da zai duba na tsanaki don yiwa kowanne ɓangare adalci.

Baba Impossible ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kokari wajen binciken tsohon gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje musamman akan wasu kura-kurai na ganganci da gwamnatin da ta gabata tayi.

Related Posts

Leave a Comment