268
Hukumar tsaron farin kaya DSS, ta ƙi amincewa da bayar da belin dakatacen Gwamnan babban bankin ƙasa Godwin Emefiele.
Emefiele ya shigar da ƙorafi a wata kotu a Abuja cewa, bai kamata hukumar DSS ɗin ta ci gaba da tsare shi ba kawo wannan lokaci, in da ya nemi kotun tasa DSS su sake shi domin samun ‘yanci da yin walwala kamar kowa.
To sai dai hukumar tsaron farin kayan ta ƙi amincewa da hakan, in da ta bayyana wa kotun cewa, idan aka saki Emefiele zai iya tserewa daga ƙasar nan, don haka sakin nasa babbar matsala ce.
Tsohon Gwamnan babban bankin dai na tsare ne har yanzu a hannun jami’an DSS da suka kama shi bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da shi a kwanakin baya.
Nafi’u Salisu daga Abuja.


