Home Labarai Yadda jirgin kasa ya Bata bat!

Yadda jirgin kasa ya Bata bat!

by masta

YADDA JIRGIN ƘASA YAYI ƁATAN DABO A YANKINMU

Mazauna Kaduna Sun Bayyana Damuwarsu A Kan Rashin Jirgin Ƙasa mai Jigila.

Wasu al’umar Kaduna da ke yankin Maraban Jos, Rigachikun da Barakallahu da ke cikin ƙaramar hukumar Igabi, da wasu jama’ar Kawo da na Sabon Tasha, sun yi kira ga Gwamnan jihar Mal. Uba Sani, a kan ya taimaki rayuwarsu ya dawo musu da jirgin ƙasar da zai ci gaba da yin jigilar mutane daga yankunan zuwa cikin gari kamar yadda ake yi a baya.

Jama’ar Kadunan sun miƙa wannan koke nasu ga Gwamna ne sakamakon halin ƙunci da aka shiga na tsadar abin hawa a dalilin tsadar man fetur.

A yayin zantawar wakilin IDON GARI da wasu al’ummar ta Kaduna da suke miƙa wannan koke nasu, sun bayyana cewa, “An ɗauki tsawon lokaci rabon da jirgin ƙasar da ke zirga-zirga a yankinsu ya dawo, wanda ga shi kuma yanzu tsadar man fetur yasa basa iya biyan kuɗin abin hawa daga unguwanninsu zuwa kasuwar Kawo da Central Market da aka fi sani da (Gari Kasuwa), domin kuɗin ya ninka abinda suke biya a baya sau kusan uku.”

Hakan yasa a wasu lokutan masu ƙaramin ƙarfi ke takawa a ƙasa daga Rigachikun da Barakallahu zuwa Kawo, yayin da wasu ma kan haƙura da fitar gaba ɗaya saboda tsadar abin hawa. Wannan ne yasa suke roƙon Gwamna ya dawo musu da jirgin yayi aikin ɗibar fasinja a yankunansu don sauƙaƙa musu tsadar abin hawa.

Al’umar wannan yanki sun ce, “A lokacin Gwamna Sir Patrik Ibrahim Yakowa, da Arc. Namadi Sambo, jirgin ƙasar yana zuwa Rigachikun ya ɗebi fasinja, sannan idan yazo Barakallahu ya tsaya ya aje ko kuma ya ɗiba zuwa Kawo a Naira 20, wanda zai wuce Central Market zai biya Naira 40, sai kuma daga Central market zuwa sabon tasha N20 shima…”

To amma tun bayan shuɗewar waɗancan tsofaffin Gwamnoni biyu, sai zirga-zirgan jirgin ƙasar a waɗannan yankuna ta tsaya, har kuma yanzu ba a dawo da jirgin ba, duk da cewar akwai jiragen ƙasar a ƙasa.

Nafiu Salisu daga Kaduna.

Related Posts

Leave a Comment