
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya shirya sake fasalta hukumar tattara kudaden haraji ta jihar domin bunkasa hanyoyin samar da kudaden shiga ga jihar. Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin wani taron gaggawa da ya kira hukumomin dake samar da kudaden shiga ga jihar a ranar Larabar nan 21 ga Yuni, 2023 da ya gudana a gidan gwamnatin jihar, Katsina.
Gwamnan ya ce babban makasudin wannan taro shi ne don kara fadakar da hukumomin dake samar da kudaden shiga da su kara matsa kaimi wajen gudanar da ayyukansu domin tattalin arzikin jihar Katsina ya bunkasa. Kan haka ne, Gwamnan ya ce akwai bukatuwar a sake fasalta ayyukan hukumomin dake samar da kudaden shiga domin su yi aiki yadda ya kamata.
Sai dai, Gwamnan ya koka kan yadda ake samun karancin bin doka wajen biyan kudaden haraji da kuma halayyar wasu jami’an tattara kudaden haraji da ya ce hakan na a sahun gaba wajen taimakawa ake samun nakasu wajen tattara kudaden shigar. A ta bakinsa, jihar Katsina na bukatar hanyoyin samar da kudaden shiga, musamman a wannan halin da ake ciki na ana dab da fara biyan basukan da aka ciyo. Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya ce kudirinsa shi ne jihar Katsina ta rika samar da kudaden da za ta biya albashin ma’aikatan jihar ba sai ta jira dauni daga Abuja ba.
Daga karshe, Gwamnan ya bukaci Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Arch Ahmad Musa Dangiwa da ya kafa kwamiti na musamman da zai yi nazari kan yadda ake samun kudaden shiga a jihar a wasu jihohin dake samun kudaden da yawa, domin Katsina ta kwaikwaye su.
SSA Isah Miqdad,
Ofishin Babban Daraktan yada Labarai.
21/6/2023.

