Daga Jaridar Sawaba
A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kai wata ziyarar ba-zata zuwa Asibitin ƙwararru na Sakkwato domin tabbatar da ingancin ayyukan da hukumar asibitin ke yi.
Malam Abubakar Bawa, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Sakkwato.
Bawa ya ce, matakin da gwamnan ya ɗauka na ziyartar cibiyoyin kiwon lafiya ba tare da bayyanawa ba ya biyo bayan jerin matsalolin da ’yan jihar suka bayyana kan rashin isar da kiwon lafiya a asibitin.
Sakataren yaɗa labaran ya lara da cewa, sauran abubuwan da suka sa gwamnan ya ziyarci asibitin sun haɗa da duba da idon basira game da gurɓacewar tsarinsa, rashin wutar lantarki, larancin ma’aikata da rashin kayan aikin kiwon lafiya da dai sauransu.
Ya jaddada cewa, Aliyu ya ziyarci asibitin ne da babur mai ƙara uku domin samun bayanai daga hannun ma’aikatansa.
Gwamnan ya ce, “Na yi mamakin abin da na gani a lokacin ziyarar da na kai asibitin wanda ya ɗauki tsawon awanni huɗu; ya ba ni damar ganin abubuwa da kaina.
“Masu lafiya da danginsu suna fuskantar kowane irin yanayi mai haɗari saboda gurɓataccen muhalli da kuma rashin kayan aiki a wuraren kiwon lafiya.
“’Yan uwan marasa lafiya sun dogara ne kawai da wasu hanyoyin samun wutar lantarki saboda rashin wutar lantarki a asibitoci.
“Na umurci mahukuntan asibitin da su gan ni don ci gaba da tattaunawa kan yadda za a magance munanan lamarin,” in ji gwamna


