315

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, a ranar Litinin, ya karbi bayanai kan ayyukan Ma’aikatu, Sashe da Hukumomi (MDA’s) na Jihar Katsina.
Taron wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar Katsina, Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ayyukan wasu hukumomi ke tafiya a halin yanzu tare da Kira ga hukumomin da su zage damtse wajen ganin an farfado da martabar aikin gwamnati a jihar Katsina.
Hukumomin da aka gana da su sun hada da, Ma’aikatar Shari’a, Ma’aikatar kula da Harkokin Noma, Ma’aikatar dake kula da Wuraren Kiwo, Hukumar kula da Asusun bunkasa noma na duniya (IFAD) da Sauran su.
SSA Isah Miqdad,
Ofishin Babban Daraktan Yada Labarai.
19/6/2023.

