
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya rusa dukkanin Kwamitocin Hukumomin Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatu, Cibiyoyi, da Kamfanonin Gwamnatin Tarayya.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwar manema labarai da ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta fitar a ranar litinin.
Sanarwar dake dauke da sa hannun Willie Bassey, darektan yada bayanai na sakataren gwamnatin kasar ya bayyana cewa,
“Rushewar ba ta shafi kwamitoci da hukumomin dake jerin Jadawali na uku, Sashi na 1, Sashe na 153 (i) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba.”
“Manyan jami’an gudanarwa na hukumomin, Cibiyoyi, da Kamfanonin Gwamnati tarayya ne za su mika al’amuran da ke bukatar kulawar Hukumarsu ga Shugaban kasa, ta hanyar Manyan Sakatarorin ma’aikatun da ofisoshi hukumomi masu sa ido.”
“Ana kuma umurtar manyan sakatarorin da su kai irin wadannan wasikun zuwa ga shugaban kasa ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Don haka, dukkan Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomi su tabbatar da bin wannan umurnin da ya fara aiki daga ranar Juma’a 16 ga watan Yuni, 2023.” Inji shi. Daga Shafin Aliyu Samba

