Gwamnati Plateau (Jos) ta saka dokar hana zirga-zirga a ƙamar hukumar Mangu. Hakan ta faru ne sakamakon yawan hare-haren ta’addanci da ‘yan bindiga suke kawowa a yankin.
Dokar ta fara aiki ne daga yau Litinin 19 ga Watan June, 2023. Sai dai dokar hana zirga-zirgar bai shafi jami’an tsaro ba, da ma’aikatan Gwamnati masu aiki na musamman da kuma masu neman labarai (‘Yan jaridu).
Jihar Plateau na ɗaya daga cikin jihohin da suke fama da ayyukan ‘yan ta’adda, wanda ko a kwanakin baya farmakin ‘yan bindigar a wasu yankunan jihar sai da ya jawo rasa rayukan mutane da dama tare da asarar dukiya mai tarin yawa.
A yanzu haka dai ƙaramar hukumar Mangu na cikin barazanar farmakin ‘yan bindiga da hakan ya haifar da tsoro gami da fargaba ga mazauna garin, duk da Gwamnatin jihar ta ɗauki matakin hana zirga-zirga.
Daga: Nafiu Salisu


