UƘUBAR DA MATAFIYA KE FUSKANTA A SAKAMAKON TSADAR MAN FETUR
Tun bayan bayyana cire tallafin mai (subsidy) da Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ta ayyana, wanda ya jawo tashin gwauron zabi da man yayi, har yanzu dai al’umma na kokawa game da wannan lamari.
Duk da cewa wannan ba shi ne karo na farko da man fetur ɗin yake ƙara kuɗi ba, to sai dai na wannan lokacin yafi kowanne ɗaga hankali da jefa al’ummar ƙasa cikin damuwa da tashin hankali, na yadda man ya tashi daga Naira 220 zuwa 560 duk lita guda.
A kan hakan ne muka zanta da wasu fasinjoji da ‘yan kasuwa har ma da Direbobi da suka bayyana damuwarsu a kan wannan hali da ake ciki na tsadar man fetur.
Wani matashin ɗan kasuwa da ke zuwa daga jihar Bauchi, ya bayyanawa wakilin IDON GARI cewa, a da kafin mai yayi tsada, ya kan zo kasuwar Kano sau uku a sati ya sayi kaya ya koma, amma yanzu da kyar yake iya zuwa sau ɗaya ma a sati, ya ce hakan ta faru ne saboda ƙarin kuɗin mota da ya ninka kusan sau biyu a kan yadda suke biya a baya. Haka nan ya ce wasu kayan sun sami ƙari a kansu, yayin da wasu kuma suke a yadda suke a da.
Ita ma wata mata da ta fito zata yi balaguro zuwa jihar Kogi, ta ce tun misalin ƙarfe shida na Asuba ta baro gida, amma sai ta je tashoshin mota uku bata samu tafiya ba saboda ƙarancin fasinja. Haka zalika matar ta bayyana cewa, a da suna biyan dubu 4,500 amma yanzu ta biya dubu 9,500 sannan zata biya kuɗin kaya daban.
A ɓangaren Direbobi kuwa, wani direba da yake jiran ayi masa lodin fasinja zuwa Kaduna daga nan Kano, yace kwanansa biyu yana layi amma saboda rashin fasinja yasa sai dai ya goge motar ya koma inuwa ya kwanta har yanzu bai samu lodi ba, saɓanin lokacin baya da har tara fasinja ake yi kafin su shigo tasha.
Shi ma wani direba da ke lodin zuwa jihar Nasarawa, ya ce kafin mai ya ƙara kuɗi yana zuba man Naira 65,000 daga Nasarawa yazo Kano ya koma, amma yanzu sai ya zuba na 95,000 zuwa da komawa. Sannan idan sun zo Kano a yanzu sai sun yi kwana biyu kafin su sami fasinja, baya ga tsadar man ya ce hatta kayan gyaran mota ma sun ƙara kuɗi.
A ƙarshe sun yi kira ga Gwamnati da su kan su dillalan man fetur kan cewa, su duba halin da al’umma suke ciki su sassauta wannan al’amari.
Daga: Nafiu Salisu

