Home Labarai Gwamna Radda ya Ayyana kudirinsa na farfado da wurin Norman Rani na Shanghai.

Gwamna Radda ya Ayyana kudirinsa na farfado da wurin Norman Rani na Shanghai.

by masta


Gwamna Radda ya ziyarci wurin shirin noman zamani na Shonghai a Mairuwa, ya ayyana kudirinsa na farfado da shi

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya sanar cewa gwamnatin jihar a shirye take ta farfado da shirin nan na noman zamani na Shonghai mai fadin murabba’in kadada 59 da ke Mairuwa karamar hukumar Faskari ta jihar.

Malam Dikko da ya sanar da hakan a karshen mako, ranar Lahadi 18/6/2023 a garin Mairuwa lokacin da yake duba cibiyar, ya yi bayanin cewa farfado da wurare irin wadannan ya zama wajibi ga gwamnatinsa a kokarin da take yi na cike gibin da take da shi a bangaren noma.

Ya yi nuni da cewa farfado da wannan cibiya da tuni gwamnatin jihar ta mallake ta a zamanin mulkin tsohon Gwamna Ibrahim Shema a shekarar 2012 domin gudanar da harkokin noma a zamanance da za ta rika kawo wa jihar kudi, zai karfafi guiwar gudanar da noman rani, kiwon kaji da sauran harkokin noma a zamanance a jihar.

Kamar yadda Gwamnan ya sanar, mayar da hankali kan samar da abinci a cikin gida, zai taimaka a rika noma abincin da zai wadaci al’umma har a kai kasuwa a sayar da daraja da hakan zai taimaka matasa su samu ayyukan dogaro da kansu.

A lokacin ziyarar, Gwamnan ya samu tarba daga mukaddashin babban sakatare a ma’aikatar aikin gona, Alhaji Abubakar Ibrahim Yar’adua, shugabannin kananan hukumomin Funtua da Faskari, Sarkin Maskan Katsina da sauransu.

A yayin ziyarar, an zagaya da Gwamnan a cikin wannan cibiya a wuraren da ake sarrafa shinkafa, kwamin kiwon kifi, matsugunin da aka samar wa ma’aikata da ofisoshin gudanar da harkokin mulki da sashen intanet na cibiyar da aka samar.

Daga cikin wadanda suka rufa wa Gwamnan baya a yayin ziyarar, akwai, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina Alhaji Jabiru Tsauri, da makusancin Gwamna Abdullahi Aliyu Turaji, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan kan kafafen sadarwar zamani, Isah Miqdad da kuma babban mataimaki na musamman ga Gwamnan kan harkokin rediyo da jaridu, Abubakar Badaru Jikamshi da sauransu.

SSA Isah Miqdad,
Ofishin Darktan yada labarai.
18/6/2023.

Related Posts

Leave a Comment