Home Labarai Uwargidan Gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Radda ta yi Kira ga Sanatoci da ‘yan majalisu kan inganta lafiya a jihar Katsina

Uwargidan Gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Radda ta yi Kira ga Sanatoci da ‘yan majalisu kan inganta lafiya a jihar Katsina

by masta

Uwargidan Gwamnan Katsina HE Zulaihat Dikko Radda ta nuna damuwarta kan kiwon lafiya al’ummar jihar Katsina.

Daga Musa Abdulkadir Bakori

Kiran ya biyo baya ne a yayin gudanar da walima wanda mutanen Musawa Matazu suka shirya ma Dan Majalisa mai wakiltar kananan hukumomin biyu Talban Musawa. A yayin jawabin nata Hajiya Zulaihat ta mika sakon godiya da bangajiya ga daukacin al’umar da suka halarci taron.

A yayin jawabin nata, mai dakin gwamnan kuma first lady ta jihar katsina ta kara da cewa ” bincike ya nuna cewa jihar katsina ce tafi kowa ce jiha samun mata masu mutuwa yayin haihuwa”. Hakan ya biyo bayane sakamakon rashin samun ingantattun kayan aiki a mafi yawoan asibitoci. Tace yin hakan zaisa a samu raguwa na mace mace da mata da keyi kullum yayin haihuwa. Ta Kuma yi alkawarin tallafawa a wannen bangare.

Daga bisani ta kara jaddada ma al’umar Musawa da Matazu cewa mai girma gwamna yana sane da halin da al’umar jihar katsina suke ciki. A koda yaushe tunanin sa shine al’umar jihar katsina. Domin shi mutum ne mai cika alkawari.

Daga karshe tayi jinjina ga Dan majalisar Musawa Matazu tare da Senator na Funtua zone Mukhtar Dan Dutse a bisa kokarin su na inganta rayuwa da kyuatata ma al’umar su.

Related Posts

Leave a Comment