Home Labarai Muhimman Shawarwarin da Halifan Tijjaniyya Sarkin Kano na 14 Khalifa Muhammadu Sunusi ya ba wa Tinubu

Muhimman Shawarwarin da Halifan Tijjaniyya Sarkin Kano na 14 Khalifa Muhammadu Sunusi ya ba wa Tinubu

by masta

Yayin ziyarar da Sarkin Kano na sha Hudu sannan Halifan Tijjaniya Muhammadu Sunusi ya Kai wa Shugaban Kasa Alh Ahmad Bola Tinubu a fadarsa a ranar 15/6/2023, ya ba wa Tinubun muhimman shawarwari Wadanda in har aka bi su za a sami cigaba a kasar nan musamman ma AREWA. Saboda dukkan Shawarwarin sun tabo muhimman abubuwan da suka mayar da kasar baya . Halifan ya kawo batun tattalin arziki da ire-iren Shawarwarin da ya rika ba wa gwamnatin ba ya da ba ta saurara ba. Ya tabo batun tsaro musamman babbar mas’alar nan ta Kanoma da makiyaya. Batun ilimin ‘ya’ya mata da ya jima yana ci wa sarkin tuwo a kwarya shi ma ya kuma jafdadawa Tinubu shi. Talauci da ya addabi Arewa shi ma Halifan ya magantu. Da dai sauran muhimman abubuwa musamman cire subsidy da mutuwar mutane 37 makiyaya. A karshe sarkin ya Fadawa Tinubu kofarsa a bude take duk lokacin da ake bukatar shawararsa. Allah ya Kara wa Halifan Tijjaniyya Lafiya Allah ya Kara ba shi kwarin gwiwa da tallafar al’umma, Amin.

Related Posts

Leave a Comment