
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda a ranar Alhamis, 15th Yuni, 2023, ya halarci babban taron majalisar kula da tattalin arziki ta kasa da ya gudana a fadar shugaban kasa ta Aso, Villa, Abuja.
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da wannan majalisa da za ta kula da tattalin arzikin kasa (NEC), inda ya bukaci mambobin majalisar da su yi aiki kafada da kafada da gwamnatinsa wajen farfado da tattalin arzikin ‘yan Nijeriya.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da majalisar, Shugaba Bola Tinubu, ya yi nuni da cewa akwai aiki babba a gaban sabuwar gwamnatinsa wajen farfado da tattalin arzikin kasa, amma dai ya ja kunnen cewa babu wani uzurin da za a yi na gaza cimma nasara, tun da dai har aka roki ‘yan Nijeriya su ba da damar ta hanyar zabe, kuma suka ba da wannan dama.
Ya yi kira ga ‘yan majalisar tattalin arzikin da su dukufa kan aiki, inda ya yi nuni da cewa ‘yan Nijeriya sun zura musu idanu su ga katabus din da za su yi. Ya kara da cewa “ina cike da tabbacin cewa mutane na tare mu, amma dai suna bukatar jin an yi garambawul kuma cikin kankanin lokaci”.
Majalisar kula da tattalin arzikin dai za ta rika zama a duk wata, sannan an dora mata alhakin ba shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki da kuma matakan da za a bi domin alkinta tattalin arziki musamman daga gwamnatin tarayya.
Mambobin majalisar sun hada da daukacin gwamnonin jihohi 36 na kasar nan, Gwamnan babban bankin kasa CBN da sauran wasu jami’an gwamnati da aka tsoma a cikin aikin.
SSA Isah Miqdad,
Ofishin Darakta Janar na yada labarai.
15/6/2023.

