
JAWABIN FARKO NA SHUGABA TINUBU A RANAR DEMOKRADIYYA
Fassarawa : Barrah Almadany
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta kasance mai aminci da gaskiya, daidaito da adalci, ya kara da cewa “zai yi mulki cikin gaskiya, mutunta doka, da jajircewa wajen kare martabar al’ummar Najeriya a ko da yaushe”.
Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su jure illar cire tallafin man fetur.
Shugaban ya ce an dauki matakin ne don ‘yantar da albarkatun ƙasa da wasu tsirarun mutane ke amfana da shi mai makon yan kasa. Wajen karkatar da kudaden zuwa aljuhunsu.
Tinubu, a jawabinsa na ranar Dimokuradiyya na farko a matsayinsa na shugaban kasa, ya ce ya yi tasiri wajen cire tallafin man fetur da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi a wani yunkuri na magance matsalar talauci a kasar nan.
A yayin jawabinsa na farko, shugaban ya bayyana cewa tallafin man fetur “ya tafi”.
Ko da yake tawagar kafafen yada labarai na shugaban kasar sun fayyace cewa za a fara aiwatar da manufar nan gaba a watan Yuni, tuni an fara aiwatar da shirin bayan tallafin, inda kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) Limited ya sanar da daidaita farashin famfo a duk fadin kasar. .
Wannan ci gaban dai ya haifar da tashin gwauron zabi na farashin man fetur, lamarin da ya kara dagula al’amura a tsakanin ‘yan Najeriya.
Da yake magana kan batun, Tinubu ya ce ya zama wajibi a dauki matakin kare kasar daga rugujewa.
Na yarda cewa shawarar za ta dora nauyi a kan talakawan mu. Ina jin zafin hakan. Wannan wata shawara ce guda daya da ya kamata mu dauka domin ceto kasarmu daga hannun wasu marassa kishin kasa.
“A cikin raɗaɗi, na roƙe ku ’yan uwana yan Najeriya, ku ƙara haƙuri ɗan sadaukarwa don ci gaban ƙasarmu.
“Don amincewarku da imaninku gare mu, ina tabbatar muku cewa sadaukarwarku ba za ta zama a banza ba.
“Gwamnatin da nake jagoranta za ta biya ku ta hanyar zuba jari mai yawa a fannin sufuri, ilimi, samar da wutar lantarki na yau da kullun, kiwon lafiya da sauran kayayyakin amfanin jama’a da za su inganta rayuwar jama’a.”
ZAN CIKA KOWANE ALKAWARI DA NA ƊAUKA
Shugaban ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa zai aiwatar da ajandar sa ta ‘Sabuwar Gwamnati , yayin da ya yi kira ga zababbun shugabannin da su yi wa ‘yan Nijeriya hidimar rashin son kai.
“A ranar dimokuradiyya ta bana, ina yi mana wasiyya da mu sake sadaukar da kanmu wajen karfafa wannan tsarin gwamnati na ‘yantattu da ke jagorantarmu cikin shekaru 24 da suka gabata,” in ji Tinubu.
“Musamman mu da muka samu damar zabe a mukamai na gwamnati a matakai daban-daban a bangaren zartarwa da na majalisa dole ne mu sake jajircewa wajen sadaukar da kai ga jama’a, da kuma samar da ribar dimokuradiyya ta hanyar da ta dace daidai da zaben mu. wannan shine alkawurin mu
“A nawa bangaren da na gwamnatina, na yi alkawarin sabunta kudirinmu na cika duk wani bangare na yarjejeniyar zabenmu da jama’a – ajandar ‘Sabuwar Gwamnati
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta kasance mai aminci da gaskiya, daidaito da adalci, ya kara da cewa “zai yi mulki cikin gaskiya, mutunta doka, da jajircewa wajen kare martabar al’ummarmu a koda yaushe”.
Fassarawa : Edita Barrah Almadany

