378
Ancigaba da rusau: Gwamnatin jihar Kano ta rushe gine-ginen da aka yi a jikin filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.
Ta kuma rushe wasu Shaguna da ke jikin makarantar Sakandire ta Ƙofar Nassarawa ta fuskar titin IBB.
Sannan ta rushe gine-ginen da ke jikin makarantun Sakandire na Duka Wuya da ta Goron Dutse.
Dukkanin wan nan aiki na rusau ya gudana ne cikin Daren jiya Asabar 10 June 2023, shin menene ra’ayin ku ? Saura wane guri kuke da bukatar a dira cikin wan nan rana kuma ?


