DJ Ya Addabi ‘Yan Islamiyya da Kida Ya Gamu da Fushin Alkali
Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a jihar Kano ta ajiye wani mai kayan sauti wati (DJ) mai suna Ali Dan-Asabe bisa zarginsa damun makarantar Islamiyya a yankin.
Kotun wacce take zaune a karamar hukumar Ungogo ta tuhumi mai kayan kidan ne saboda yana kawo cikas ga Islamiyyar wurin hana karatun yara tafiya yadda ya kamata.
An gurfanar da Ali Dan-Asabe a gaban kotun bayan samun korafi daga hukumar makarantar kan cewa karar kidan nasa yana kawo cikas ga daliban makarantar da kuma dauke musu hankali akan karatunsu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito mai gabatar da kara, Sifeta Bashir Wada ya fada wa kotu cewa karar abin kidan na Dan-Asabe yana hana yaran sauraron abin da malamansu ke koya musa a cikin aji.
“Lokacin da hukumar makarantar ta same shi akan lamarin, Ali ya ce ba zai rage karar sautin kayan kidan ba, madadin haka sai ya kara sautin kayan kidan nasa.”
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin tuni ya amince da zargin da ake yi masa.
Alkalin kotun, Munzali Idris Gwadabe ya umarci a tsare Ali da kuma dage sauraran karar zuwa ranar 6 ga watan Yuli don ci gaba da shari’ar.


