Home Labarai Na Tabbata zan dawo da Nijeriya Cikin Hayyacinta. Cewar Shugaban Kasa Tinubu

Na Tabbata zan dawo da Nijeriya Cikin Hayyacinta. Cewar Shugaban Kasa Tinubu

by masta

Na Tabbata Zan Dawo Da Najeriya Cikin Hayya Cinta, Cèwar Sabon Shùgaban Kasa Alhaji Asiwaju Bola Ahmad Tinubu

DAGÀ Bashir Abdullahi El-bash

Tinubu ya ce yana da hanyar da za ta sake ɗaukaka Najeriya da kuma kawo ci gaba ga kowa da kowa, ya ƙara da cewa “Zan iya tafiyar da hanya zuwa wadata, na san hanyar ilimi domin na yi imani da shi, na san hanyar da za a magance matsalar rashin tsaro. ƙasar.”

Sai dai ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ba shi damar yin aiki ta hanyar hakuri da taya shi addu’ar fatan yin nasara.

Ya ce, “Za mu yi aiki tare ne domin ba za mu koma lokacin da ake tari ba, ba za mu bari a yi mulkin kama karya ba.”

Related Posts

Leave a Comment