Home Labarai Shehu Atiku Sanka Masani Uban Masana

Shehu Atiku Sanka Masani Uban Masana

by masta

Malamai Magada AnnabawaTare da
Bilkisu Yusuf Ali

An haifi shehu Abubakar Atiku Sanka dan Halliru danAbubakar dan Musa (Mairisala) a garin Katsina a shekarar 1896. Mahaifinsa malam Halliru da kakansamalam Abubakar duk haifaffun Katsina ne.Ammamahaifin kakansa Mallam Musa (Mairisala) ya zo ne daga qasar Tunis shi da jama’arsa , shi ya sa ake cemusu Rumawa. Dalilin kiransa da Mairisala kuwa shine malamin fiqhu na farko da ya kawo littafin risalaqasar Hausa lokacin da ya je aikin Hajji ya gamu da ‘yan’uwansa Larabawan qasar Tunis sai ya fanshetadaga wajensu ya taho da ita qasar Hausa ya kuma yadata.

Shehu Abubakar Atiku ya girma a hannun ‘yar’uwarkakarsa mai suna Rahmatu (Yaya Babba) matar malamAbba dan Fannah a Dandalin Turawa da ke Kano. Ta dalilin kulawarta ne har ya yi karatun alqur’ani a hannun mijinta. An shaidi Rahmatu da mace ce maiibada da tsananin da riqon addini. Jajirtacciya mai bintafarkin xariqar Tijjaniya sau da qafa. Sannan maizartaccen Imani cikin Shehu Ahmadu Tijjani. Ita ce ta tsaya tsayin daka a tarbiyyarsa har zuwa lokacin da Allah ya yi mata rasuwa a shekarar 1972.

Shehu Atiku ya fara da karatun al-qur’ani a hannunmijin kakarsa Malam Abba Dan Fanna haka ya yiahalari da kurdabi da alburda da Badamasi duk a wajensa. Daga nan sai ya koma da karatu a wajenShaihu Muhammadu Salga xan Alhaji Umaru inda yakaranci risala da Iziyya da arshada ta ibn Rushidi da Mukhtasarul Khalil har zuwa babin aure, ya kumakaranta littattafan aqida kamar su MuqaddamatulBurhamiyya ta Imamu Sunusi da Aqidatul wusxa da sauransu. Ya karanci littatafan dariqa kamar su Su’alwal jawab na shehu Muhammadu Salga da Yaqutulfaridah na shehu Nazifi. Ya ci gaba da neman ilimi a fannoni da dama kamar tafsiri da Hadisi da harshen Larabci inda ya karanci littattafan Alfiyya ta xan Malik da Ajrumiyya da Mulhatul I’irab da sauransu.

Shehu Atiku ya zurfafa iliminsa da nean ilmai a fannonin fiqhun dariqa da tasawwuf da sauranfannonin harshen Larabci a wajen Shehu AbubakarMijinyawa Baqin ruwa. Ya karanta littafai kamar hakaa gun Shehu Mijinyawa kamar su Jawahirul ma’any da Durratul Kharidah ( Sarhin Yaqutatul Faridah) da Bugyatul mustafida na shehu Arabi da Alfiyatultasawwuf ta shehu Mustapha da sauran littattafai da dama

Shehu Atuku Sanka ya karbi xariqar Tijjaniya a hannunShehu Muhammadu Sanka a shekarar 1916. Sannan yayi tarbiyyar Ruhi a hannun Shehu Abubakarmijinyawa.

Shehu Atiku na Shehu bai tsaya a karatun littattafai ba, a’a har da barshen Larabci saboda shi ne harshen da malamai kan yi muhawara da shi a tsakaninsu a garinKano a wancan lokacin. Ya karanta ilimin hisabi a wajen Muhammadu dan Ajurum da Mulhatul-irab ta Imamu Hariri mai littafin muqamah da sauranlittattafan da suka shafi adabi da lugga (Harshe) da kuma qa’idojin Larabci.

Shehu Atiku na daya daga cikin manyan shaihunnanmalamai na garin Kano da ma Afrika baki daya wandatarihi ba zai taba mantawa da sunansa da gudummawarsa musamman a garin Kano da Najeriyada ma Afrika baki daya. Shehi Atiku ya kasanceShaihin dariqa wadda ya yi mata hidima jini da tsokada tunaninda da lokacinsa da ruhinsa. Shehu Atiku yawallafa litttattafai da daman gaske wadanda a qiyasiana da tabbacin sun haura casa’in tun daga na rubutunzube da rubutattun waqoqi wanda ma fi yawa sunaMagana ne a kan al’amuran addini da harshen larabcida kuma sufanci. A taqaice rubuce-rubucensa sun kasugida uku wato Sufanci da Adabi da kuma Fiqhu.

Babu shakka Shehu Atiku ya yi gagarumin qoqarin da ba za a raina ba dangane da rubuce-rubucensa litattafaiya kuma tsara waqoqi a harshen Hausa da Larabci a kan abubuwa daban-daban. Misali ya rubuta waqoqina:

Yabon Annabi SAW

Yabon Shehi Tijjani

Yabon Shehi Ibrahim Inyass

Wa’azi da gargaxi

Aqida

Ibada

Da sauransu

Daga cikin waqoqinsa akwai

• Waqar amsar mai tambaya a cikin ma’aloli da yawa.
• Tusamma
• Taimakon Daqiqi
• Asma’u zatil jamali
• Matserar mata
• Nasiha ga ‘yan’uwa
• Yabon fiyayyen halitta
• Arziqin masoya
• Tarihin kwaki
• Begen Muhammadu
• Rakaxa’u

Shehu Atiku Sanka yana da madaukakiyar daraja a wajen malaman amaninsa musamman ta bangarorinilimai daban-daban tare da qarfin hujja da kwarewawajen bincike da gogewa wajen hujja da fasahar zance. Kuma ya nutse aa cikin ilimin sanin dariqar Tijjaniyyahakan ta sanya ya himatu da darussan ta da bincike a kanta har sai da ya zamana ba shi da wanda za a kwatanta shi da shi a wannan fanni. Shehu Atiku yanacikin manyan Sahabban Shehu Ibrahim Inyas.

Shehi Atiku malami ne da har a qarshen rayuwarsayana neman sani, mai haquri da rashin gazawa da kyauta da xaukar nauyi. Gidansa ya zama sansani naneman sani inda almajirai ke zuwa daga ko’ina a fadinqasar nan har da Nijar.

Daga cikin Almajiransa akwai:-

Shehu Balarabe Jega

Shehu Ibrahim Alti Funtua

Shehu Ahmad Abulfathi Maiduguri

Shehu Muhammadu Jibiya

Shehu Yahya Jibiya

Shehu Muhammadu Birnin magaji

Shehu Ibrahim Qaya

Shehu Adamu Katibi

Shehu Imrana Damari

Allah ya yi wa Shehi Atiku rasuwa ranar laraba 9 gawatan rabi-ul thani 1394 Hijiriyya. Yana dan shekaru64 an binne shi a maqabartar Gwauron dutse . A yanzuKhalifan Shehu Atiku Shi ne Shehu Tuhami sannandaga cikin ‘ya’yansa Akwai Dr Lawi Atiku da DrSunusi Shehu Atiku da Sheikh Makiyyu Atiku.

Related Posts

Leave a Comment