APC A YAU
BREAKING NEWS ; GWAMNA AHMED ALIYU YA DAKATAR DA WADANSU MANYAN ABUBUWA 6 JIHAR SOKOTO.
1- An soke dukkanin Kantomomin riko da sauran kwamitocin riko dake kananan hukumomi 23 a jihar Sokoto, An umurci Kantomomin su mika mulkin ga Daraktocin mulki dake yankunan su
2- An soke dukkanin canza sunayen wadansu manyan makarantun gaba da Sakandari da tsohon Gwamna Aminu Tambuwal yayyi a Sokoto.
3- Duk wani nadin sarauta da karin girma ga ma’aikatun gwamnati wanda tsohon gwamna Aminu Tambuwal yayyi a wadansu makonni da sunka gabata, Gwamna Dr. Ahmad Aliyu ya dakatar dasu.
4- An dakatar da duk wani Gwanjon kayan gwamnati da Aminu Waziri Tambuwal yayyi, har sai an sake dubawa.
5- An soke duk shuwagabannin Hukumomi da ma’aikatun gwamnati nan take.
6- An soke dukkanin filayen Gwamnati da abinda ke kama da wannan wanda tsohuwar Gwamnati ta sayar.


