Home Labarai Gwamnan Jihar Katsina Dr Dikko Umar Radda ya Karrama marubuta da suke yi nasara a gasar rubutun ka gaggun labarai a jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Dr Dikko Umar Radda ya Karrama marubuta da suke yi nasara a gasar rubutun ka gaggun labarai a jihar Katsina

by masta

ADABI MUDUBIN RAYUWA

RUBUTU DA MARUBUTA

An Yi Taron Bada Kyaututtukan Rubutu A Katsina.

A jiya Alhamis 25 ga watan Mayu, 2023 a ka gudanar da gagarumin bikin raba kyaututtuka na rubutun gajerun labarai ga marubuta maza da mata, wanda aka shirya ƙarƙashin jagorancin Jarman Kankia Arc Ahmed Musa Ɗangiwa FNIA, FICEN.

Taron ya gudana ne a babban ɗakin taro na Local Government Service Commission, da ke kan titin zuwa Kaita jihar Katsina, wanda aka fara gudanar da shi da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

Haka kuma an ƙaddamar da littafi mai suna ƊAUKAR JINKA, wanda ya ƙunshi labarai daban-daban da marubuta maza da mata suka wallafa labaransu a ciki.

Marubuta maza da mata daga ciki da wajen jihar Katsina da suka shiga gasar rubutun daga mabambanta wurare, sun rabauta da kyaututtuka na kuɗi da takardar shaidar yabo. Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake shirya irin wannan gasar rubutu ga marubuta ba, dake gudana a ƙarƙashin Jarman Kankia Arc Ahmed Musa Ɗangiwa.

Taron na jiya, ya samu halartar manyan baƙi da dama, da suka haɗar da Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, zaɓaɓɓen gwamnan jihar mai jiran gado, Mal. Dikko Umar Raɗɗa PhD, da Justice Musa Ɗanladi Abubakar (babban mai shari’a na jihar Katsina), da Maigirma Sarkin Daura, Alh. Umar Faruƙ Umar, Professor Kabir Ibrahim Matazu, da sauran manyan masu faɗa a ji a ciki da wajen jihar Katsina.

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment