
An sayar da kujerun Alhazanjihar Kano sama 180 ba bisa Ka’ida ba.
Jaridar Alfinjir tta rawaito cewa ‘ Sabon shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Alhaji Lamin Rabi’u Dan Bappa ya ce daga lokacin da aka naɗa shi shugabancin hukumar, zuwa yanzu ya samu badakala da dama da aka aiwatar a hukumar.
Daga cikin abubuwan da aka aikata na son zuciya sun haɗar da siyar da kujeru sama da 180 wadanda babu su ga maniyyatan Kano.
Lamin ya bayyana hakan lokacin da yake karbar ragamar shugabancin hukumar a hannun tsohon shugabanta Muhammad Abba Danbatta.
Hakan ya faru ne a yammacin Alhamis a harabar hukumar.
An dai zargi Muhammad Dambatta da nuna kiyayya ga gwamnati Abba Kabir Yusuf a bayyane, kuma hakan ya sanya da aka rantsar da Abba Kabir ya fara da tsige shugaban hukumar tare da maye gurbin sa da nasu na jam’iyyar NNPP.

