Home Labarai Tinubu Ya yi Alkawarin Cika Burikan ‘Yan Nijeriya

Tinubu Ya yi Alkawarin Cika Burikan ‘Yan Nijeriya

by masta


TINUBU YA SHA ALWASHIN CIKA BURUKAN ƳAN NIJERIYA.

Daga: Hassan Munammed Marke

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin tafiyar da mulkin sa a tsarin da ƙal’ummar ƙasa zasu ci moriyarsa, yana mai duba da irin girman nauyi da ya rataya a kansa yayin da ya karɓi lambar girmama a matsayin shugaban ƙasa na gaba.

Ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa na karɓar lambar girmawa mafi ƙololuwa ta ƙasa wato GCFR wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa masa fadar shugaban ƙasa.

Zaɓaɓɓn shugaban ƙasar ya ƙara da cewa ‘yan Najeriya sun cancanci samun ci gaba fiye da yadda suka tsinci kawunasu a ciki, inda yayi alƙawarin neman shawarar shugaba Buhari a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya zama mutum na 16 wanda aka bai wa lambar girmamawar ta GCFR bayan jerin shugabannin baya, kama daga Nnamdi Azikiwe da Obafemi Awolowo da Shehu Shagari da, Olusegun Obasanjo da Abdulsalami Abubakar sai Ibrahim Babangida, da Ernest Shonekan, sai Sani Abacha da Umaru Yar’Adua da Goodluck Jonathan sa’annan Moshood Abiola.

Shugaba Buhari ya kuma naɗawa zaɓaɓɓen mataimakin shuagban ƙasar Kashim Shettima lambar girmamawa ta GCON.

Related Posts

Leave a Comment