286
Yayin bude katafaren kamfanin matatar Mai da Dangote ya bude ba a ga gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ba a wurin bikin, duk kuwa da wannan gawurtacciyar masana’antar abin alfaharin Kanawa ce tunda dansu ne. Kuma a wannan gabar ta rigegeniyar bude aiki a karshen wa’adin mulkin masu barin gado al’ummar jihar Kano ba ta yi zaton gwamnan zai ki zuwa haka kawai ba. Duk da wasu suna ganin ko dai ya samu labarin Kwankwaso zai halarta ne? Tambayar ita ce me ya hana Ganduje zuwa ?lallai akwai dalili.


