Home Labarai Ruwan Sama ya yi Ta’adi a Jihar Bauchi

Ruwan Sama ya yi Ta’adi a Jihar Bauchi

by masta

GUGUWA DA RUWAN SAMA A BAUCHI

Yadda Jama’ar Misau Suka Haɗu Da Iftila’in Guguwa Da Ruwan Sama.

Wata guguwa da ruwan sama mai ƙarfi sun lalata gidaje da gine-ginen Jama’a sama da guda ɗari biyu (200) a garin Misau, hedikwatar ƙaramar hukumar Misau ta jihar Bauchi.

Jama’ar garin na Misau sun bayyanawa manema labarai cewa, guguwa da ruwan saman sun tashi hankulan jama’a, ta yadda suka gaza yin wani yunƙuri don ganin sun sami wani ɗauki.

Tuni dai masana suke ta kiraye-kirayen al’umma a kan a kula da kyau ayi hattara game da daminar bana, saboda za a iya samun mamakon ruwan sama da aka daɗe ba a taɓa ganin irinsa ba.

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment