758
Sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya baiyana cewa hukumar na aiki tuƙuru don ganin an rage farashin aikin hajjin 2025, wanda ake kiyasin zai kai Naira miliyan 10.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Farfesa Usman ya ce ba fatan NAHCON ba ne kuma hukumar ba ta bukatar a ce maniyyatan Hajjin badi sun biya Naira miliyan 10 kudin aikin Hajji.
Ya kara da cewa fatan hukumar, a karkashin shugabancin sa shi ne alhazai su biya kudin aikin Hajji ƙasa da Naira miliyan 8.1 da su ka biya a Hajjin 2024.
Ya kuma yi fatan cimma wannan bukata cikin yardar Allah.


