Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan yadda aka gudanar da zabukan shuwagabannin jam’iyyar a wasu jihohi 12 ciki har da jihar Katsina, a zabuan shuwagabannin jam’iyyar da aka gudanar a dukkanin fadin jihohin Nijeriya.
Sakataran yada labarai na jam’iyyar PDP ta kasa baki daya Debo Ologunagba ya ce ana cikin gudanar da bincike kan korafe-korafen da suka karba game da wasu jihohi amma har yanzu ba a kai karahe ba
Kamar Yadda majiyar Katsina Daily News ta rawaito, sakataren yada labaran ya kara da cewa akwai korafe-korafen shigar da kara da wasu ɓangarori suka yi game da zabukan, da sauran wasu korafe-korafe da aka rubuto masu a jihohi 12, ciki har da jihar Benue, Katsina, Kogi, Ekiti, da jihar Rivers inda korafinsu na gaban NWC yanzun haka
A jihar Rivers bangaren Wike da gwamnan jihar kowane na tutiyar cewa shike da jam’iyya.
Haka abin yake a jihar Katsina, inda za a iya cewa, jam’iyyar ta rabu tsagi biyu, tsakanin sanata Yakubu Lado Danmarke, wanda ya tsaya wa jam’iyyar a zaben gwamna na shekarar 2023 da ya gabata, da kuma tsagin Dr Mustapha Inuwa tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina da ya sauya sheka ya dawo PDP bayan ya sha kasa a zaben fitar da gwani na dan takara gwamna a jam’iyyar APC
A satin da ya gabata Katsina Daily News , tsagin Sanata Lado Danmarke sun shiga zaben jam’iyyar, inda kuma dan takarar shugabancin jam’iyyar na bangarensu Nura B Amadi Kurfi ya lashe zaben a matsayin zaɓaɓɓen shugaban jam’iyyar PDP ta jihar Katsina.
Sai dai tsagin Dr Mustapha Inuwa sun daka tsalle sun ce ba ta sabau, bindiga a ruwa, an tauye masu hakkinsu na tsayawa takara a jam’iyyar wajen han su sayen fom din nuna sha’awar fitowa takarar, hakan ne ya sa suka garzaya kotu suka shigar da kara tare da kauracewa inda aka gudanar da zaben, domin suna kallon zaben a matsayin ya saba wa doka kuma baya bisa ka’ida


