DAGA Bashir Abdullahi El-bash
Biyo bayan ajiye aiki da babban mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu, Ajuri Ngelale yayi a yau, ƴan Najeriya na Kiraye-kiraye ga shugaban ƙasa da ya karrama mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa, Malam Abdulaziz Abdulaziz da wannan matsayi duba da cancantarsa.
Ƴan Najeriya sun bayyana Malam Abdulaziz Abdulaziz a matsayin gogaggen ɗan jarida masanin aiki wanda ba za a ji kunya ba idan ya hau wannan kujera duba da abubuwan da yayi cikin shekara ɗaya a aikin da aka ba shi.
Yayi amfani da ƙwarewarsa wajen yaɗa ayyuka da duk wani motsin nasarar shugaban ƙasa gami da kare kima da darajar shugaban ƙasa da gwamnatinsa.
Wannan tasa ƴan Najeriya da dama ke ganin ba wa Malam Abdulaziz wannan kujera tamkar ƙara masa ƙarfin gwiwa ne kan ayyuka nagari da yake yi. Sannan kuma hakan tamkar fitar da yankin Arewa kunya ne da ƙara ɗaga darajar shugaban ƙasa da siyasarsa.
Domin kuwa a cikin shekara ɗaya, Malam Abdulaziz yayi abin da waɗanda suka shekara takwas a baya ba su yi ba a wannan matsayi duba da cewa ya samar da tsare-tsare na tallafawa matasa da jan su a jika da ba su kulawa da muhimmanci da ɗanɗana musu zaƙin gwamnati.
Malam Abdulaziz mutum ne mai kykkyawar mu’amala. Ba shi da ƙyashi, duk wata dama idan ta samu yana ƙoƙarin ganin ya jawo al’umma sun amfana batare da bambancin yanki, addini, ko ƙabila ba. Ba shi wannan matsayi na babban mai magana da yawun shugaban ƙasa zai taimaka wajen haɗa kan al’ummar Najeriya musamman ƴan Arewa tare da ƙarawa shugaban ƙasa farin jini da karɓuwa a babban zaɓen 2027.






