Fadar shugaban kasa ta umurci sabon shugaban hukumar alhazan Nijeriya Professor Abdullahi Saleh Usman ya shiga ofis a matsayin mukaddashin shugaban hukumar ta NAHCON kafin sanatoci su dawo hutu su tabbatar da nadin da Shugaba Tinubu ya yi masa a watan da ya gabata