Home Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Najeriya ta baiwa yan kasuwa wata guda su rage farashin kayayyaki ko su fuskanci hukun ci

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Najeriya ta baiwa yan kasuwa wata guda su rage farashin kayayyaki ko su fuskanci hukun ci

by masta

Hukumar kula da kasuwanci da ingancin kayyaki FCCPC ta sanya wa’adin wata guda ga ‘yan kasuwa domin rage farashin kayayyaki a fadin Najeriya.

Hukumar ta sanar da wa’adin wata guda ga ‘yan kasuwar ne bayan ta tura jami’an ta sun shiga kasuwannin sun gano yadda yan kasuwa ke tsawwala farashin kayayyaki,

Mista Tunji Bello, wanda shi ne sabon mataimakin shugaban hukumar FCCPC, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron kwana guda da masu ruwa da tsaki suka yi kan farashi da riba, wanda ya gudana ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce da zaran wa’adin ya kare za su dauki gagarumin hukunci kan yan kasuwa kungiyarsu da daidaikunsu da kamfanonin da aka kama suna tsawwala farashi.

Me zaku ce?

Related Posts

Leave a Comment