339
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya magantu kan sake tsayawar takarar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
A cewar Sani, kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa kowane dan Nijeriya damar tsayawa takara.
Shehu Sani ya bayyana hakanne yayinda yake tattaunawa da ‘yan jarida a Kaduna, yace “A nawa ra’ayi, ya kamata a bar ma ‘yan Kudu ko shin shugaban kasa Bola Tinubu ne, Peter Obi ko kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, domin Arewa ta samu shugaban kasa a 2031


