Home Labarai YANZU-YANZU: Najeriya ta kulla yarjejeniya da kamfanin kera jiragen sama na ƙasar Amurka, Boeing -inji ministan Sufuri Festus Keyamo

YANZU-YANZU: Najeriya ta kulla yarjejeniya da kamfanin kera jiragen sama na ƙasar Amurka, Boeing -inji ministan Sufuri Festus Keyamo

by masta

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Festus Keyamo, ya ce Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfanin jiragen sama na Amurka, Boeing, domin bunkasa ci gaba mai dorewa a fannin sufurin jiragen sama na kasar.

Ministan, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa, yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ƙasashen ta ƙunshi tsare-tsare da dama, da suka haɗa da bayar da horo ga Najeriya kan jagoranci da raya fannin sufurin jiragen sama na Najeriya da kuma taimakawa kamfanonin jiragen sama a kasar wajen bunkasa sha’anin sufuri daidai da zamani.

Related Posts

Leave a Comment