Home Labarai Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya yi bankawana da jami’ar Al-Qalam na dan wani lokaci sakamakon samun Shugaban hukumar alhazai na kasa

Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya yi bankawana da jami’ar Al-Qalam na dan wani lokaci sakamakon samun Shugaban hukumar alhazai na kasa

by masta

A ranar Talata 27/08/2024 ne Prof. Abdullahi Saleh Pakistan ya jingine Aikinsa na wani lokaci na koyarwa a Jami’ar Al-Qalam dake garin Katsina.

Jingine Aikin yana daga cikin shirye shiryen fuskantar Jagorancin da Maigirma Shuganam Kasa Bola Ahmad Tunubu ya bashi na Jagorantar Hukumar Aikin Hajji ta kasa wato (NAHCON)

Malam ya gabatar da jingine aikin nasa a Office din Shugaban Jami’ar Farfesa Nasiru Musa Yauri

Hakika Malam ya samu yabo daga wajan abokanan aikin sun yabesa Sosai.

Daga Karshe sunyiwa Malam Addu’a Allah ya bashi ikon Sauke Nauyin da aka dora masa
Malamin ya sami kyakkyawan yabo daga Jami’ar da yake koyarwa tunda daga Malamai har zuwa Dalibai da Ma’aikatan Jami’ar. A nasa jawabin Shugaban hukumar alhazan na kasa Farfesa Pakistan ya yi godiya ga shugaban jami’ar ta Al-Qalam Prof Yawuri da Malamai bisa ba shi goyon baya da suka yi a Yayin gudanar da aikinsa sannan ya Nuna yadda yake kishin jami’ar in da ya ki yarda ya je wasu Jamioin saboda kishin Al-Qalam Kuma Kara da cewa "ba zai taba mantawa da Jami’ar Al-Qalam ba tabbas Jami’ar ta bashi gudun mawar da ba zai taba mantawa da ita ba, domin a cikinta ne ya zama Professor.

Malam yace Jami’a har guda biyu na Federal Government sun ba shi katin gayyata domin ya koma can da aiki kuma Mukamin da yake da shi a Jami’ar Al-Qalam Amma ya ki amincewa.

Hakika Jami’ar Al-Qalam tana raina ko ina cikinta ko nayi nesa da ita.

An yi wa Malam Addu’a kan Allah ya yi masa jagora ya yi rigo da hannayensa.

Tabbas Malam ya zauna da kowa Lafiya a wajan aikinsa don haka kowa ke Nuna alhinin rabuwa da shi inda wasu suka Yi ta zubar da hawaye.
ABDULLAHI NAGEGIME

Related Posts

Leave a Comment