Home Labarai Mai Martaba Sarkin Kano Ya yaba da nadin Farfesa Abdullahi Sale Pakistan a matsayin shugaban Hukumar Alhazai Ta Kasa..

Mai Martaba Sarkin Kano Ya yaba da nadin Farfesa Abdullahi Sale Pakistan a matsayin shugaban Hukumar Alhazai Ta Kasa..

by masta

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yaba da nadin Farfesa Abdullahi Sale na Pakistan a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa, yana mai bayyana hakan a matsayin wanda ya cancanta.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya fitar, Sarkin ya
bayyana irin gogewar da Farfesa Sale yake da ita a harkokin aikin Hajji, ciki har da shugabancinsa na hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci Farfesa Sale da ya yi amfani da kwarewarsa wajen bunkasa martabar hukumar alhazai ta kasa da kuma inganta muradun Najeriya a tsakanin al’ummar musulmin duniya.

Sarkin ya kuma yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan nada dan jihar Kano kan wannan matsayi mai daraja, inda ya bayyana fatan Farfesa Sale ya zama babban jakadan jihar Kano da Najeriya.
Daga Kabiru Haruna.

Related Posts

Leave a Comment