Home Labarai 28 August, 2024 15:25

28 August, 2024 15:25

by masta

NERC ta bai wa jihohi shida ƙarfin gudanar da harkokin lantarki

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar gudanar da wutar lantarki ta Ƙasa, NERC ta bai wa jihohi shida ƙarfin gudanar da kasuwancin lantarkin yankunansu a wani yunƙuri na samar da ci gaba a harkar ƙasuwancin lantarki.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta sanya a shafinta na X, ta ce ta bai wa jihohin Enugu, Ekiti, Ondo, Imo, Oyo da Edo lasisin gudanar da harkokin kasuwancin lantarkinsu.

Hakan na zuwa ne bayan da jihohin suka samar da hukumomin gudanar da lantarkinsu wanda hakan ya ba su matsayin kula da ɓangaren a yankunansu.

NERC ta bayyana cewa, ci gaban ya samu ne bisa umarnin miƙa ragamar lantarkin jihohin daga gare ta zuwa sabbin hukumomin gudanar da lantarki na jihohin (SERCs).

Bugu da ƙari, tun a watan Afrilu ne hukumar ta sanar da cewa za ta bai wa huɗu daga cikin jihohin ragamar kula da harkokin lantarkinsu wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu, 2024. Daga jarida Manhaja.

Related Posts

Leave a Comment