629
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar katsina Rt. Hon. Nasir Yahaya, ya jagoranci sauran mambobin majalisar ya zuwa fadar gwamnati domin bakarka da zuwa ga gwamna malam Dikko Umar Radda
Rt.Hon. Nasir Yahaya ya jaddada aniyar majalisar wajan cigaba da haɗa hannu da sashen zartaswa, ta hanyar goyon bayan gwamna a kokarin da yake na inganta rayuwar al’umma.
Shugaban majalisar ya kara da cewa ba zasu gajiya ba wajan fadawa gwamna gaskiya akan lamurran dake damum al’umma musamman a bangaren tsaro da kuma hanyoyin da za’a bi domin magance matsin rayuwa da al’umma ke ciki.
Gwamna Radda yayi farin ciki da wannan ziyara inda yayi godiya matuƙa bisa ga dimbin goyon bayan da yake samu daga majalisar dokokin.






