Da zuciya mai nauyi, ina mika ta’aziyyata ga iyalan marigayi Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammed Bawa, da mutanen Karamar Hukumar Sabon Birni baki daya, da kuma dukkan al’ummar jihar Sokoto bisa rasuwarsa da wannan rashi wanda mukayi na Sarkin Gobir wanda masu garkuwa suka kashe shi cikin rashin imani.
Yanayin da ya haifar da mutuwar marigayi sarki tabbas abin takaici ne, rashin imani, rashin tausayi, kuma abin tir ne, kuma hakika abu ne wanda zamubi matakai don hukunta masu laifi.
Na samu labarin rasuwar hakimin gundumar cikin tsananin baƙin ciki. Ya kasance mutum mai addini, gaskiya, amana, da son zaman lafiya wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa mutanensa da kuma daukacin bil’adama.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya ba marigayi sarki matsayi mafi girma a Aljanna Firdaus kuma ya ba iyalansa da dukkan mutanen Karamar Hukumar Sabon Birni hakurin jure wannan babban rashi da mukayi.
Gwamnatina ta kuduri aniyar amfani da dukkan hanyoyin da ake da su wajen kawar da ta’addanci. Ina rokon mutanen jihar su tallafa wa hukumomin tsaro da bayanan da suka dace domin kawar da wannan annoba.
Ina kira ga mutane su ci gaba da yin addu’a ga Allah Madaukakin Sarki domin taimakawa gwamnati wajen kokarinta na kawar da ta’addanci da sauran laifukan da ke addabar jihar.
Ina kira ga hukumomin tsaro a jihar su kara himma wajen tabbatar da tsaron jihar a kowane lokaci da kuma tabbatar da cewa masu laifin wannan muguwar kisa sun fuskanci cikakken hukunci kuma hukunchi mai tsanani.


