Gwamnatin Tarayya ta ofishin hukumar kula da tace man fetur ta Ƙasa, NMDPRA ta aika saƙon gargaɗi ga gidajen man fetur da ke tsananta wa kwastomomi inda wasu ke sayar da lita a farashin da ya kai Naira 1,000.
Hukumar ta zargi wasu ƴan kasuwa masu zaman kansu da ke ɓata ƴan Nijeriya ta hanyar sayar da lita ɗaya a tsakanin Naira 900 zuwa 1,000 wanda ya haura kuɗin da ƙasa ta ƙayyade.
Hakan ya haifar da koke-koke acikin al’umma wanda ya kai ga samun cinkoso a gidajen mai da dama a Nijeriya.
La’akari da yadda ake sayarwa a gidajen man NNPCL inda a ke samun lita a tsakanin Naira 568 da 617, saboda haka ne a ke samun layukan ababen hawa don neman rangwame ga masu saye.
Saidai ƴan kasuwa masu zaman kansu sun koka kan yadda su ke samo man fetur daga defo na ƴan kasuwa a farashi mai tsanani wanda a wasu lokuta ya kan kai Naira 850 duk lita ɗaya.
Amma, mai magana da yawun NMDPRA, George Akume Ene-Ita, ta ƙalubalanci iƙirarin da ƴan kasuwan suka yi, ta na mai cewa su na da kundin bayanai na defo-defo da ke nuna cewa a ƙasa da haka sosai a ke sayan man.
Game da batun gidajen mai da ke sayarwa akan 900 zuwa 1,000 a jihar Legas da wasu jihohi, ta ce za a gaggauta rufe ire-irensu matuƙar ba su daina ba.
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI


