Home Labarai Gwamnatin tarayya za ta samar da shiri makamancin NYSC ga waɗanda suka kammala NCE

Gwamnatin tarayya za ta samar da shiri makamancin NYSC ga waɗanda suka kammala NCE

by masta

Ma’aikatar ci gaban matasa ta ce tana shirin samar da wani tsarin bada horo mai kamanceceniya da shirin bautar ƙasa, NYSC, ga daliban da suka kammala karatun NCE.

Karamin ministan matasa, Mista Olawande Wisdom, ne ya bayyana hakan a yayin bude gasar BEMORE a garin Ibadan na jihar Oyo a ranar Litinin.

Acewar kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ministan yayi bayanin cewa, ma’aikatarsa na hadin gwiwa da ma’aikatar ilimi wajen aiwatar da yin garanbawul kan shirye shiryen bada horo ciki har da samar da tsarin horaswa makamancin NYSC ga masu NCE.

Ya bayyana cewa, a yayin da shirin NYSC an yi shi ne ga wadanda suka kammala jami’o’i, ba zai zama daidai ga wadanda suka kammala NCE ba.

"Abin da ma’aikatar nan tafi baiwa muhimmaci shi ne ‘yan kasa da basu horo, muna da shirin NYSC ga wadanda suka kammala jami’o’i, amma ya batun wadanda suka kammala NCE da sauransu?".

" Muna son mu kafa tsarin bada horo, don haka babu bukatar kaje wata jihar. Zaka yi ne a iya jihar ka", inji ministan.

Related Posts

Leave a Comment