Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya buƙaci hukumar samar da wutar lantarki a yankunan karkara, (REA) da su ƙara ƙoƙari su tabbatar kowane ɗan Najeriya ya samu wutar lantarki a kowane loko da saƙo.
Shettima, yayi wannan kira ne a ranar Juma’a a lokacin da tawagar hukumar, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Abba Abubakar Aliyu ta ziyarce shi a ofishinsa domin gabatar masa jadawalin tsare-tsaren ayyukansu.
Sannan kuma, ya amince da buƙatarsu ta shiga cikin haɗin gwiwa da majalissar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) domin su riƙa samun damar ƙulla alaƙar aiki da gwamnoni tayadda wutar lantarki za ta kai kowane loƙo da saƙo na Najeriya. "za mu ba ku cikakken haɗin kai da goyon baya domin ganin wutar lantarki ta je ko’ina a Najeriya". In ji Kashim Shettima.
A yanzu haka ma, hukumar ta (REA) ta samu tallafin kuɗi kimanin Dala Miliyan 750 daga bankin Duniya da na raya Afrika domin ayyukan samar da wutar lantarki a yankunan karkara.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci hukumar da ta riƙa sanar da al’umma duk wasu ayyukansu da nasarorin da suke cimmawa ta hanyar amfani da kafofin sadarwa na Rediyo da talabijin gami da sabbin kafafen sadarwa na zamani duba da cewa yanzu haka mutane ba sa sanin abin da suke yi kan ayyukansu.






