Home Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Equatorial Guinea Mbasogo Sun Rattaba Hannu Kan Yerjejeniyar Iskar Gas Ta Tsibirin Guinea.

Shugaba Tinubu Da Shugaban Equatorial Guinea Mbasogo Sun Rattaba Hannu Kan Yerjejeniyar Iskar Gas Ta Tsibirin Guinea.

by masta

Ayammacin Larabar 14 ga watan Agustar 2024 ne Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aikin bututun iskar gas na Gulf of Guinea, tare da kara kulla dankantaka tsakanin kasashen biyu.

A jawabin da ya yi a taron rattaba hannun, shugaba Tinubu, wanda ya ke rangadin kwanaki uku a kasar Equatorial Guinea, ya ce rattaba hannu kan yarjejeniyar zai bude wasu sabbin damammaki na hako iskar gas da kuma samar da ayyukan yi.

Shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi samar da ayyukan yi, abinci, da kuma jaddada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, sai kuma duba hanyoyin warware rikice-rikice da ke addabar nahiyar Africa da suka yi wata ganawar sirri gabanin rattaba hannu kan yarjejeniyar.

"Maimakon sanya ido muna kallon rikice-rikicen dake addabar kasashen nahiyar mu irinsu Jamhuriyar Kongo, dole ne mu yi aiki tare don magance matsalolinmu da kanmu," in ji shugaba Tinubu.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa tattaunawarsu da shugaban kasar Equatorial Guinea ta kuma shafi kalubalen tsaro da walwalar cinikayya a yankunan Afirka da kuma samar da abinci.

A nasa jawabin, shugaban kasar Equatorial Guinea ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakanin kasarsa da Najeriya ta shekaru da dama, kuma a wannan lokacin akwai bukatar zurfafa hadin gwiwa a fannonin da suka dace.

Shugaba Mbasogo ya ce manufar Afirka na samun kujera ta dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na da matukar muhimmanci ga ci gaban nahiyar, yana mai tabbatar da cewa Equatorial Guinea za ta yi aiki tare da Najeriya don cimma wannan manufa.

Shugaban Equatorial Guinea ya ce rattaba hannu kan yarjejeniyar kunshe yake da dabarun ci gaban Afirka.

Daga Sabuwar Najeriya

Related Posts

Leave a Comment